Jamus za ta bai wa Labanan kudaden karfafa tsaro
January 10, 2024Jamus za ta bai wa Labaran Euro miliyan 15, da za a yi amfani da su domin bai wa sojoji damar inganta tsaro a kudancin kasar, daidai lokacin da rikici ke kara ta'azzara tsakanin Isra'ila da 'yan tawayen Hezbollah.
A jawabin da ta yi a Beirut babban birnin kasar Labanan a wannan Laraba, ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce gwargwadon taimakon da dakarun wucin gadi na Majalisar Dinkin Duniya suka samu a Labanan, gwargwadon su ma na kasar za su samu.
Minista Baerbock wadda ta bukaci da a dakatar da kai wa juna hare-hare a iyakar Labanan da Isra'ila, ta yi kiran kwance damarar yaki a tsakanin bangarorin duka biyu.
Cikin kalamanta dai ta ce bai kamata yaki da Isra'ila ke yi kan kungiyar Hamas a Gaza, ya zamo hujjar kunna sabuwar wuta ta rikici a yankin ba.