1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ci gaba da horas da sojin Mali

April 21, 2021

Gwamnatin Jamus ta kara adadin sojojinta zuwa 600 a Mali tare da tsawaita aikinsu a kasar. Wannan ya zo a lokacin da cibiyar SIPRI da ke nazari kan tsaro ta ce sauyin yanayi na shafar ayyukan kiyaye zaman lafiya a Mali.

https://p.dw.com/p/3sKVt
Bundeswehr in Mali
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

A sabon rahoton da ta fitar, cibiyar SIPRI mai bincike na musamman kan harkokin da suka shafi tsaro da zaman lafiya na kasa da kasa ta gano yadda sauyin yanayi ya taka rawa sosai na ba wa rikicin kasar Mali sabon salo. Cibiyar ta ce rashin tsaro da ake fama da shi a kasar ya shafi albarkatun kasa da na ruwa har da sauran albarkatu da al'umma ke dogaro da su, matakin da ya dada tsananta yunkurin tabbatar da zaman lafiya.

A karin bayani ga DW kan yadda sauyin yanayin ya shafi ayyukan zaman lafiya, Dr Farah Hegazi ta cibiyar SIPRI na cewa: "Illar sauyin yanayi yana sa aikin wanzar da zaman lafiya tafiyar hawainiya, saboda yawancin mutanen Mali sun dogara ne kan albarkatun kasa wajen rayuwarsu ta yau da kullum. Duk lokacin da sauyin yanayi ya gurgunta harkar noma, kenan zai shafi  samun mutane. Misali yankunan masu karancin sana'aoi, ana ba su zabin shiga ta'addanci don samun abinci. Amma idan ana samun isassshen ruwan sama, to akwai saukin masu shiga irin wadannan kungiyoyin."

Dürre in der Sahel Zone Naturkatastrophen Flash-Galerie
Tsaro ya tabarbare a arewacin Mali sakamakon koma bayan noma da kiwoHoto: picture-alliance/ dpa

 Yankunan da ke arewacin kasar Malin sun dade a hannun 'yan tawaye tun bayan kwace iko daga hannun gwamnati, abin da ya haddasa tsaiko wajen aiwatar da manufofin yaki da sauyin yanayi a bangaren gwamnati, musamman samar da dabarun ayyukan yi.

A cewar Dr Farah Hegazi ta cibiyar SIPRI: "Akwai karancin dama ga 'yan Mali na shiga harkokin kasuwanci baya ga sana'ar kiwo da suka saba, wannan ya tilasta mutane da dama shiga gurbatattun ayyuka irin fatauci da mutane. Kasuwanci abu ne mai matukar wahala a arewacin Mali, abin da ke dada tsananta rayuwa. Wannan ya sa wasu da dama ke rungumar duk abin da ya zo musu."

Sabon rahoton cibiyar ya maida hankali ne kan dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD wato MINUSMA, wadanda aka girke da niyyar taimaka wa gwamnatin Mali yaki da ta'addanci da ma sauran kasashen na yankin Sahel tun a shekarar 2013, ko da yake aikin sojojin na karewa a watan Yunin wannan shekara ta 2021.

Mali Bundeswehreinsatz Symbolbild
Sojojin kasashe da dama na taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro a MaliHoto: Getty Images/A. Koerner

 Yanzu haka dai wasu kasashe akalla 50 sun jibge sojoji 13,000 da 'yan sandan 1,900 a kasar Mali da ke yammacin Afirka. Sai dai a gefe guda ana zargin kasar da rashin katabus na warware rikicin siyasar kasar, wanda ake ganin yana bude kofa ga matsalolin ta'addanci.