Jamus za ta mayar wa Najeriya da kayan tarihi
December 15, 2022Talla
Darakta janar na hukumar adana kayayakin tarihi na Najeriya Abba Isa Tijani na daga cikin wadanda suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar mayar wa Najeriya kere-keren tagulla da suka fito daga masarautar gargaji ta Benin a 1897. Amma Jamus ta shirya mayar da wadannan kayayyakin Najeriya a shekarar 2023 mai zuwa kamar yadda gwamnatin Jamus din ta sanar.
Ko baya ga kayayyakin tarihin masaurautar Benin, akwai wasu da yawansu ya haura dubu da dari daya da ke jibge a gidajen adana kayayakin tarihi 20 a Jamus. Sai dai bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar bar wa birnin Cologne wasu kayayakin tarihi 37 a matsayin aro na tsawon shekaru 10.