Jamus zata gudanar da ayyukan raya ƙasa na miliyoyin Euro a Masar
August 12, 2011Jamus zata karkatar basussukan Masar wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa. An cimma wannan yarjejeniya ce yau, a ganawar data gudana tsakanin ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da takwaransa na Masar Mohammed Amr a birnin Berlin. Ɓangarorin biyu sun rattaba hannu a yarjejeniyar da Jamus, tare da tuntuɓar gwamnati, zata yi amfani da euro miliyan 240 na basussukan da suka rage, wajen gudanar da ayyukan raya cigaban kasa cikin shekaru huɗu masu gabatowa.
Westerwele ya ce" wannan matakin al'ummar kasar na neman sauyi abun sha'awa ne. Mu jamusawa da tarihin yadda muka cimma democradiyyar mu da juyin juya hali cikin kwanciyar hankali, muna bada goyon bayanmu wa mutanen Masar, kuma muna yabawa irin karfin hali da al'ummar suka nuna wajen nemar wa kasarsu democraɗiyyi".
Kazalika ministocin harkokin wajen na Jamus da Masar sun yi alkawarin aiki tare domin gano bakin zaren warware rikicin Izraela da Palasdinu, tare da kira ga bangarorin biyu dasu koma teburin shawarwari. Kazalika Westerwelle da Arm sun yi kira da a gaggauta kawo karshen rigingimun kasar Siriya.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu