Janar Tchiani ya rusa majalisun jihohi da na yankuna
April 5, 2024A cikin wata dokar mai dauke da sa hannun shugaban da aka karabnta a kafar talabijin din kasar Janar Tchiani ya rusa majalisun mashawartan da ke rike da mukaman ne tun a shekarar 2020, ba tare da wani karin haske kan dalilan gwamnatinsa na daukar matakin ba.
Karin bayani : Kotu ta umarci sojojin Nijar su saki dangin Bazoum
Tuni ma dai shugaban ya dauki matakin maye gurbisu da wasu galibi sojoji da 'yansanda da wasu daidaikun fararen hula galibi masu alaka da sojojin da ke jan ragamar mulki.
Karin bayani : Niger na kara daukar matakai a kan Faransa
Wasu manya-manyan biranen kasar ciki har da Yamai da ke karkashin jagorancin wani kusa a jam'iyyar Hama Amadou, a yanzu zai kasance ne karkashin jagorancin soja in ji sanarwar da aka karanta a kafar yada labarun gwamnati.