1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Janye shiga yajin aiki

Uwais Abubakar Idris SB/MA
October 2, 2023

Kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun yanke shawarar dakatar da shirin da suka yi na shiga yajin aikin gama gari farawa daga ranar Talata, amma za su tunkari gwamnatin.

https://p.dw.com/p/4X3kb
Najeriya I Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a birnin Abuja
Zanga-zangar kungiyoyin kwadagon NajeriyaHoto: Uwais/DW

Kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun yanke shawarar dakatar da shirin da suka yi na shiga yajin aikin gama gari farawa daga ranar Talata, amma za su tunkari gwamnati don batun tsarin aiwatar da karin da aka yi masu na kudi Naira dubu 35 na tsawon watani shida kafin a kaiga yi masu karin albashi.

Karin Bayani: Zanga-zangar kungiyoyin kwadagon Najeriya

Majalisun zartaswa na kungiyoyin kwadagon Najeriyar ta Trade Union Congress da kuma NLC da suka kamala wani wani taro a Abuja, sun yanke hukunci ne na dakatar da yajin aikin na gama gari wanda suka dade da daka yajinsa suka sha, har ma da raba goron gayyata ga mabobinsu da ke jihohin Najeriyar, don nuna fushi a kan matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na zargin cika alkawari tun bayan janye tallafin man fetir. Comrade Nuhu Abbayo Toro shi ne sakataren kungiyar klwadago ta TUC wanda za su ci gaba da nazarin halin da ake ciki.

Najeriya | Zanga-zangar kungiyoyin kwadago
Zanga-zangar kungiyoyin kwadagon NajeriyaHoto: Abraham Achirga/REUTERS

An dai kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriyar da wakilan kungiyoyin ma'aikatan, domin da farko gwamnatin ta dage kan amfani da matakin kotu kafin ta kama gaskiya inda ta yiwa tayi na kara masu Naira dubu 35 na tsawon watani shida. Tuni ‘yan Najeriya suka mayar da murtani a kan wannan mataki.

Kungiyoyin dai sun nuna damuwa a kan batun aiwatar da Karin da aka yi masu musamman a matakin jiohohi da ma sauran ma'aikatan da ke kamfanoni masu zaman kansu abinda ya Sanya sake komawa ga gwamnatin kafin su rattaba hannu a kan yarjejeniyar tare da jawo hankali a kan matatun man kasar.

Yanzu dai wakilan kungiyoyi suna canm sun shiga wani taro da jami'an gwamnatin Najeriyar domin samun tabbaci a kan batun cika alkawari na aiwatar da Karin albashin, da batun albashi na malaman jamio'I da suke bin gwamnatin albashi na watani shida, wanda batu ne da za'a ci gaba da jijiyar wuya a kansa.