1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: 01.11.2024

Usman Shehu Usman
November 1, 2024

Jaridun sun ambato yadda kamfanonin hako man fetir ke kokarin ficewa daga Najeriya da batun yakin Sudan, sai kuma kasar Habasha inda rikice-rikice na kabilu ke karta yaduwa.

https://p.dw.com/p/4mUns
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta soma sharhin ne Inda ta yi labarinta kan yadda kamfanonin hakar mai ke kokarin ficewa daga Najeriya. Jaridar cewa ta yi abin takaici ne. A takaice dai jaridar na cewa kamfanin Shell da ke hakar mai a Najeriya cikin shekaru da yawa a yanzu ya sanar da cewa zai fice daga Najeriya, wato ya bi sahun kamfanin hakar mai na Exxonmobil. A cewa Frankfurter Allgemeine Zeitung, faduwar darajar Naira shi ne dalilin da ya sa kamfanonin ba sa iya jurewa asarar jarinsu a Najeriya, kuma matakan gyaran da shugaba Tinibu ke dauka ba su kaiga nuna alamar yin wani tasiri.

Südsudan Renk | Sudanesische Flüchtlinge fliehen vor dem Konflikt im Sudan
Hoto: LUIS TATO/AFP

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi ne kan rikicin kasar Sudan, jaridar ta ce ta jiyo sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Guterres  na cewa Sudan na cikin tashin hankali tamkar a marfki abin ke faruwa," in ji shi, amma tura rundunar aikin samar da zaman lafiya ba zai yiwu ba. A cewar IOM, miliyoyin mutane da suka rasa muhallansu sakamakon yakin basasa a Sudan, akwai 'yan gudun hijira kusan miliyan 14, in ji kungiya rmai  kula da 'yan gudun hijira ta duniya.  Musamman mata da yara duk ko yaushe suna kan gudu. Sojoji sun kashe fararen hula fiye da 120 a Sariha. Yakin basasa a Sudan tsawon shekara guda da rabi, sojojin kasar Sudan dai suna fafatawa da dakarun sa kai na RSF wanda kuma ko wane bangare ake zarginsa da aikata laifukan yaki.Jaridar Die Zeit ta ce garin da kusan za a iya cewa aka gina bisa yashi da kuma mazaunansa ke da alfahari da shi. A sansanin 'yan gudun hijira na Adré da ke a kasar Chadi, fiye da mutane 200,000 ba su da komai. Duk da haka, abubuwa da yawa suna aiki da kyau.

Äthiopien Gedenken an die gefallenen Soldaten in Tigray
Hoto: Million Hailesilassie/DW

A mokbciyar Sudan wato kasar Habasha, can din ma labarin ba mai faranta rai ba ne, inda jaridar Neue Zürcher Zeitung  ta ce, Eh za a iya cewa yakin ya kare, amma duk da haka kasar Habasha tana wargajewa.  Rikice-rikice na kara yaduwa a yankuna da dama na wannan kasa ta Gabashin Afirka. Wadanda ke tserewa rikicin kabilanci suna ci gaba da kasancewa a garuruwa da tantuna, amma masu bayar da agaji basa iya isa wajen don taimakon mutane sabo da rashin tsaro.Ko da a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, lokaci zuwa lokaci yara kan taru don yin wake-wake da ke nuna irin takaicinsu bayan rasa garuruwansu da yaki ya tilasta musu.