1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Daurin rai da rai ga shugaban kama karya

Mohammad Nasiru AwalJune 3, 2016

Hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban Chadi da halin da ake cikia yankin Niger Delta a Najeriya sun dauki hankalin jaridun jamus.

https://p.dw.com/p/1J07E
Tschad Diktator Hissene Habre
Hoto: picture-alliance/dpa

Za mu bude filin sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa.

Kawo karshen shari'ar da aka yi wa tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Chadi Hissene Habre da wata kotu ta yi a birnin Dakar na kasar Senegal, gagarumin cigaba ne da ya zo shekaru 26 bayan faduwar gwamnatinsa. Kuma an yi adalci ga wadanda suka tsira daga ta'asar tsohon shugaban da alkalumma suka ce yana da hannu a kisan da aka yi wa mutane kimanin dubu 40 a tsawon mulkinsa na shekaru takwas daga 1982 zuwa 1990. Kotun dai ta yanke wa Habre hukuncin daurin rai da rai a gidan maza. Jaridar ta kara da cewa shari'ar na da muhimmanci na tarihi kasancewa a Afirka aka yi ta karkashin kuma alkalan wannan nahiya da ke zama shaida cewa su ma 'yan Afirka na da kwarewar da za su iya yi wa kansu shari'a maimakon a kotun kasa da kasa ta birnin The Hague.

Ita ma jaridar Neues Deutschland ta buga labari game da shari'ar tana mai cewa hukuncin da wata kotu musamman ta nahiyar Afirka ta yanke wa tsohon shugaban Chadi Hissene Habre ya sha yabo kuma ya samu karbuwa kwarai da gaske. Fata shi ne hukuncin ya zama darasi ga sauran shugabannin kama karya a nahiyar ta Afirka.

Cikas ga aikin hako man fetur a Najeriya

Masu tada kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a tarayyar Najeriya inji jaridar Die Tageszeitung, inda ta kara da cewa:

Öl Industrie in Nigeria
Yawan kai hari kan bututan mai na jawo wa Najeriya babbar asaraHoto: picture-alliance/dpa

Yayin da yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya fada sabon rikicin sabbin 'yan tawaye masu fasa bututan mai, wasu 'yan Biafra ne kuma suka gudanar da zanga-zangar tunawa da kafa kungiyar Biafra da a shekarar 1967 ta yi shailar ballewa daga tarayyar Najeriya, lamarin da ya janyo yakin basasar tsawon shekaru uku da ya yi sanadin mutuwat fiye da mutane miliyan daya, kafin sojojin Najeriya su sake kwace yankin a 1970. Zanga-zangar ta farkon mako ta janyo asarar rayuka da dama. Jaridar ta kara da cewa hakan ya zo ne daidai lokacin da su ma tsagerun kungiyar Niger Delta Avengers ke cigaba da fasa bututan mai, abin da ke barazanar durkusar da aikin hako mai a yankin.

Matsalar yunwa a Malawi sakamakon sauyin yanayi

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta leka kasar Malawi, daya daga cikin kasashen kudancin Afirka da sauyin yanayin nan na El Nino ya fi shafa.

Malawi Markt Preissteigerung
Karancin cimaka ya haddasa hauhawar farashin kayan abinciHoto: Reuters/M. Hutchings

Jaridar ta ce fiye da shekaru 30 ke nan Malawi ke fama da fari sakamakon rashin ruwan sama, lamarin kuma da ya janyo mata karancin abinci musamman ma masara da ke zama muhimmin abinci ga al'ummar kasar. Ko da yake hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato WFP tare da Amirka suna samar da tan-tan na hatsi domin rage radadin matsalar yunwa, amma kamar yadda Hausawa kan ce sabo turkan wawa, ga al'ummar Malawi idan ba masara suka ci ba to a gare su ba su ci abinci ba. Saboda haka yanzu hukumar ta WFP ta fara yekuwar wayar da kan al'umma da nufin sauya tunaninsu dangane da nau'o'in abincin da suka saba ci.