1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu ranar sake farfado da Nigeria Airways

September 1, 2023

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da shirin kamfanin sufurin jiragen saman kasar da ta kadammar na Air Nigeria, tare ma jinginar da tashoshin jiragen sama guda biyu da gwamnatin da ta gabata ta aiwatar.

https://p.dw.com/p/4VrKX
Hoto: Osodi Emmanuel/IMAGO

Bayan kwashe tsawon lokaci ana takadama a kan wannan batu na kafa sabon kamfanin jiragen saman Najeriyar na Air Nigeria, wanda jim kadan bayan kadammar da shi a Abuja jirgin sama guda ya yi batan dabo dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki. Fara kakaba a kan abubuwan da suke da sarkakiyar gaske a wannan fani na sufurin jiragen sama sun hada da dakatar da shirin jinginar da tashoshin jiragen saman kasa da kasa na Abuja da Kano. Mr Festus Keyamo ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya bayyana dalilan daukar wannan mataki a yanzu: ''Dama akwai batutuwa da dama a kan wannan batu tun ma kafin in kama aiki a matsayin minister, daga batun kamfanin jiragen sama na Naigeria Air da kuma  jinginar da tashoshin jiragen sama biyu, don haka na dakatar da duk wannan har sai na yi bincike na kuma yi wa shugaban Najeriya bayani''.

Makomar samar wa ‘yan Najeriya kamfanin sufurin jiragen sama na kasar don kawar musu da takaici

Nigeria | Port Harcourt International Airport
Hoto: George Osodi/AP Photo/picture alliance

Kwararru a fanin sufurin jiragen saman Najeriyar dai sun dade suna nuna ‘yar yatsa a kan daukacin al'amarin. A yanzu da aka dauki wannan mataki menene makomar samar wa ‘yan Najeriyar kamfanin sufurin jiragen sama na kasar don kawar musu da takaici na matsalolin sufurin jiragen sama da suka dade suna fuskanta? Captain Bala Jibril kwararre ne a fanin sufurin jiragen sama a Najeriyar.Haka dai ta kai ga cimma ruwa na daukan wannan mataki, domin ta kai ga majalisar wakilan Najeriyar da ta gudanar da bincike a kan wannan batu tare da kiran a dakatar da shi  bisa cewa akwai rufa-rufa da ma zargi na zamba cikin aminci. Sanata Kawu Sumaila dan majalisar datawan Najeriyar ya bayyana abinda ya sanya suka nemi a dauki wannan mataki. To sai dai tsohon mnistan Hadi Sirika ya ce akwai bukatar fahimtar abubuwan da suka faru a game da kafa kamfanin jirgin saman na Air Nigeriada kwanaki kalilan bayan kadamar da shi jirgin ya yi batan dabo A yanzu ina makomar wannan lamari ga Najeriyar da ake yi wa kalon ta gaza samar da kamfanin sufurin jirgin sama na kanta?