Juyin mulki a Afrika gazawar dimukuradiyya
September 22, 2023Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 wanda ke gudana a birnin New York na kasar Amurka, inda ya ce Afrika na fama ne da salon mulki da aka tilasta mata yi amma kuma wanda bai dace da tsarin al'adun nahiyar ba.
Karin bayani: Juyin mulki na dab da zama yayi a Afirka
Kanal Mamady Doumbouya ya kuma kara da cewa wannan salon mulki ya ba wa wasu kasashe damar wawushe arzikin kasashen Afrika tare kuma da karfafa ci hanci da rashawa a tsakanin shugabannin kasashen nahiyar.
Karin bayani: Kalubalen aikin hakar uranium a Nijar
Shugaban ya karkare yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi la'akari da hakkokin kasashen Afrika, a kuma ba wa nahiyar matsayinta, kana kuma a daina yin wasan yara da al'ummomin Afrika a wannan lokaci da kan mage ya waye.
Karin bayani: Tasirin juyin mulkin Nijar a jaridun Jamus