1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Rawar da ECOWAS ko CEDEAO

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 3, 2022

Sannu a hankali ana samun karuwar yunkurin juyin mulki da ma shi kansa juyin mulkin sojoji a kasashen Afirka ta Yamma, duk kuwa da matakan da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ke dauka na ladabtarwa.

https://p.dw.com/p/46UWA
Ghana Accra | Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma | ECOWAS/CEDEAO
Yawaitar juyin mulki, na neman zamewa yankin yammacin Afirka ruwan dareHoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Kasar Mali ce dai ta fara bude kofar yin juyin mulki, inda sojoji suka kifar da gwamnati har sau biyu a cikin kasa da shekaru biyu. Bayan da sojojin Malin suka tsaga suka ga jini, sai takwarorinsu na Guinea Conakry da Burkina Faso suka biyo baya. Ba a jima ba kuma, suma takwarorinsu na Guine Bisau suka yunkura domin ganin sun kwace gwamnatin. Sai dai kuma yunkurin na sojojin Guinea Bisau ya ci tura, domin kuwa ba su samu nasarar kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo ba.

Wannan matsala dai na kara kamari a Afirka ta Yamma, duk kuwa da kokarin da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yankin wato ECOWAS ko CEDEAO ke yi na hukunta sojojin da suka kifar da gwamnati ta hanyar kakaba musu takunkumi. Koda a Alhamis din wannan makon ma, shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO sun gudanar da taron gaggawa a Accra fadar gwamnatin kasar Ghana domin nemo mafita kan yawaitar juyin mulkin da ke neman zamewa yankin karfen kafa.