Mali: Takaddama da uwargijiya Faransa
February 1, 2022Tun da farko akwai 'yar tsama ta rashin jituwa tsakanin Faransar da Mali danagane da sojojin haya da Mali ta dauko daga Rasha da Faransa domin kula da aikin tsaro na kasar, saboda suna zargin gazawar sojijin Faransan da ke kasar shekaru da dama wajen gaza shawo kan matsalar yaki da ta'adancin da ya yi katutu. Tun a shekara ta 2013 sojojin na Faransa suke Mali, bayan kwato yankin arewacin kasar daga hannu mayakan 'yan ta'adda a shekara 2012. Kasar ta Faransa dai na kallon wannan al'amari a matsayin wani sabon abu da ba ta saba gani ba, wanda shi ne karon farko da wata kasa da ta yi wa mulkin mallaka ke bujere mata har aka kai ga yin hannun riga.
Ministan harkokin waje na Jamus wanda kasarsa ke da dakaru a Mali cikin rundunar yaki da ta'addanci tare da rundunar kasashen Turai Takuba, ya ce matakin sojojin Mali na korar jakadan Faransa Joel Meyer bai dace ba. Kakakin gwamnatin na Faransa Gabriel Attal ya ce sojojin rundunar Takuba na Turai za su iya aiki a Mali har karshen watan Fabarairun da muke ciki, sai dai ya ce a karshen wata zasu kaurace su mayar da Malin saniyar ware. Farfeser Alexander Stroh Steckelberg malamin kimiyyar siyasa a jami'ar Bayruth, ya ce kasashen Faransa da Jamus bakinsu daya. A cewarsa, Jamus za ta iya goyon bayan duk wani mataki da Faransa ta dauka a kan Mali. A tsakiyar watan Janairun da ya gabata dai, ministan tsaro na Jamus Christine Lambrecht ya yi shelar cewar ba za su janye sojoji daga Mali ta barwa sojojin haya na Rasha wuri ba.