Nijar: Kaddamar da makarantar horon soja
October 3, 2024Wannan makaranta dai, za ta horas da manyan sojoji da sauran bangare na manyan jami'an tsaro. Jamhuriyar ta Nijar dai ta jima dauke da wannan buri na samar da wannan makaranta da za ta rage babban dogaro na manyan sojojin kasar na zuwa wasu kasashen ketare, domin samun cikamakin horo na babban soja. Kaddamar da wannan makaranta babban ci-gaba ne a fannin horo na manyan sojojin Nijar, wanda ta hanyar wannan makaranta suke samun dukkanin horon zama manyan sojoji da ake kira da Turancin Faranasa da (Officier Supérieur). A yanzu makarantar, ta buda kofofinta ga dalibai kimanin 26 da suka hada da manyan sojoji da jandarmomi da manyan jami'an da na fasa kwabri da ma manyan jami'an tsaron fararar hula na ma'aikatar cikin gida da harkokin waje. Da yake tsokaci kan wannan batu Farfesa Dicko Abdourahamane masani kan harkokin tsaro da yaki da ta'addanci ya ce, bude wannan makaranta wata babbar dama ce ga sojojin Nijar da sauran jami'an tsaron kasar. Baya ga manyan sojojin Nijar din, wannan makaranta ka iya karbar dalibai sojoji na kasashe aminanta musamman na kungiyar AES da suka hada da Nijar din da Mali da kuma Burkina Faso.