1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Muhawara don kare hare haren ta'addanci

Salissou Boukari
September 19, 2024

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fararar hula da masana harkokin tsaro na ci gaba da muhawarori da kuma kira ga hukumomi don daukar matakan tsaro don kauce wa afkuwar irin harin ta'addancin da ya auku a Bamako na kasar Mali

https://p.dw.com/p/4krPv
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

'Yan Magana dai na cewa mai son abinka ya fi ka dabara, kuma kan wannan batu na tsaro tun bayan harin da aka kai a birnin Bamako na kasar Mali da ke a matsayin daya daga cikin kasashen kawance na AES, al'umma a Nijar ke ci gaba da tafka muhawara a kafofin sadarwa ko shafukan sada zumunta domin ci gaba da daukar matakan tsaro.

Karin Bayani:Sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100

Wasu Sojojin Nijar
Wasu Sojojin NijarHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Duk da cewa wadannan 'yan ta'adda na kara nuna nacewarsu ta ganin sun kulla makarkashiya ta kai hare-haren ba zata domin haifar da rudani a tsakanin al'umma. Tun watanni da suka wuce duk wanda ya lura da birnin Yamai zai ga cewa akwai matakan tsaro inda dare da rana jami'ai ke bincikar duk abun da basu yarda da shi ba, kuma a cewar Bana Ibrahim na kungiyar Front Patriotique masu nuna kishin kasa sun yarda da matakan da hukumomi ke dauka a manyan biranen Nijar:

Karin Bayani: Nijar ta sanar da gano masu kulla makarkashiyar hari kan bututun manta

Dama dai a birnin Yamai, duk wata mahadar hanyoyi masu ayyukan sa kai na tsaro na farin kaya na haduwa domin sa ido kan duk wani motsi na masu ababen hawa don ganin me ke wakana kuma suna wannan aiki ne kafada da kafada da jami'an tsaro a cewar shugaban masu wannan sintiri

Wasu sojojin Nijar
Wasu sojojin NijarHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Da yake magana kan batun samar da tsaro a manyan biranen Nijar, Alhaji Daouda Tamkama mataimakin shugaban kungiyar MNSP 'yanci ta farar hula ya ce masu mugunyar akida na amfani da salo iri-iri.Sai dai daga nashi bamgare Abdoul Nasser Saidou daya daga cikin yan fafutuka da ke nazari kan harkokin yau da kullum a kasar ta Nijar na ganin cewa sai fa an koma tsari na tsaro tun na gadin-gadin :

Abin jira a gani shi ne sauyin da al'umma za su kawo a ciki lamuransu na yau da kullum a fannin bada hadin kai ga jami'ai masu aikin tsaro a duk inda suke inda ake kuma ake bukatar duk wani matafiyi ya kasance ko gida ko daji yana rike da katinsa da ke nuni da shi wanene ko daga ina yake.