Matakan kare yaduwar corona a Najeriya
December 24, 2021Ci gaba da karuwar mutanen da ke kamuwa da kwayar cutar Omicron ta cutar Covid 19 ne ya sanya kara jadada wadannan matakai da ma bullo da wasu sabbi, inda mahukunatn Najeriyar suka bayyana cewa sun yi hakan ne don katse hanzarin cutar da ke ci gaba da yaduwa a tsakanin al'umma,.
Shugaban kwamitin yaki da cutar Covid 19 a Najeria ya bayyana cewa matakan sun hada da takaita taruwar jama'a zuwa mutane 50 a wuri guda da tabbatar da tazara a tsakanin jama'a da kuma sanya takunkumi na rufe hanci da baki a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Kwararru a fanin kula da lafiyar jama'a dai sun bayyana cewa kwayar cutar Omicron din tafi saurin yaduwa a tsakanin jama'a fiye da sauran danginta na Delta da Alpha da suka rigata bayyana, abinda ya sanya fuskantar karuwar yaduwarta a Najeriya da a rana guda an samu fiye da mutane dubu hudu sun kamu. Dr Muktar Mohammed babban jami'i a kwamitin yaki da cutar ta Covid 19 ya bayyana cewa suna taka tsan tsan ne don har yanzu kwararru suna bincike a kan nau'in Omicron na Covid 19 din.
Daya daga cikin matakan da zasu yi wahala ga jama'a shi ne na shawarar takaita mutanen da zasu kai ziyara a tsakanin iyalai a lokacin wannan biki.
A yayin da halin koma bayan tattalin arziki da rashin tsaro ya hana mutane da dama tafiya garuruwansu na asali da bisa al'ada can suke bikin Kirsimeti, wadannan matakai zasu kara rage armashin bikin Kirsimeti a bana, to sai dai tsaron kaya yafi ban cigiya.