1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Libiya: Bincike a kan ambaliyar ruwa

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 29, 2023

Babban mai shigar da kara na Libiya Al-Seddik al-Sour ya bayar da umurnin cafke karin wasu jami'an gwamnati hudu, kari a kan takwkas din da aka kama a Litinin din da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4WzG2
Libiya | Derna | Ambaliya | Satumba
Mutane da dama ne suka halaka a mabaliyar ruwan Libiyan ta wannan wata na SatumbaHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance

Da ma a Litinin din da ta gabata babban mai shigar da karar na Libiya Al-Seddik al-Sour da ke zaman mai shigar da kara na bangaren gwamnatin da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita a kasar, ya bayar da umurnin kama jami'an gwamnati takwas ciki har da magajin garin Derna da ambaliyar Ruwan ta yi wa barna wanda kuma aka sallame shi daga aiki bayan afkuwar ibtila'in. A ranar 10 ga wannan wata na Satumba da muke ciki ne dai aka samu mahaukaciyar guguwa da aka yi wa lakabi da Storm Daniel a yankin gabashin Libiya, inda ta haddasa ambaliyar ruwan da ta halaka mutane dubu uku da 893 yayin da wasu dubbai suka yi batan dabo.