1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Libiya: An futar da tsammanin samun masu rai

Abdourahamane Hassane Abdoulaye Mamane
September 16, 2023

Kwanaki bayan mummunan iftila'in da ya samu yankin Derna na kasar Libiya, masu aikin ceto sun fara debe tsammanin samun raguwar mutane masu rai a yankin.

https://p.dw.com/p/4WQWc
Masu aikin ceto na dauke da wata gawa a Derna
Masu aikin ceto na dauke da wata gawa a Derna Hoto: Ayman Al-Sahili/REUTERS

Kwanaki shida bayan mumunar guguwar da ta hadasa ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar dubban rayuka a Libiya, a yanzu da alama babu wata shaidar samun wasu jama'ar da ake zaton sun makkale a cikin baraguzan gine-ginen da suka ruguje.

Karin Bayani : Tagwayen bala'o'i a kasashen Afirka biyu

Libyen I Unwetter - Tausende Tote erwartet
Hoto: Ibrahim Hadia al-Majbri/XinHua/picture alliance

Guguwar Daniel, wacce ta afka wa yankin Derna, mai yawan al'umma dubu 100,000 dake a gabashinLibya a daren ranar Lahadi zuwa Litinin, ta  kai ga katsewar wasu madatsun ruwa guda biyu, lamarin da ya haifar da ambaliyar mai girman tsunami tare da rafin da ke ratsa birnin, wanda ya kwashe duk abin da ke cikin hanyarta.

Karin Bayani: Libiya: Likitocin ketare sun kawo dauki

Ministan kiwon la fiya na Libiyar Othman Abdeljalil,  ya ce ya zuwa yanzuu mutane 3166 ne suka mutu, kana ya yi gargadi game da yadda ake bayyana wasu alkalluman da ya ce ba gaskiyya ba ne.