1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Dangote na bayar da hadin kai ga EFCC

January 7, 2024

Runkunin kamfanin Dangote a Najeriya ya ce yana bayar da hadin kai ga binciken hukumar EFCC kan amfani da kudade ketare ba bisa ka'idar babban bankin kasar ba.

https://p.dw.com/p/4axGL
Shugaban rukunin kamfanin Dangote a Najeriya, Aliko Dangote
Shugaban rukunin kamfanin Dangote a Najeriya, Aliko DangoteHoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency/picture alliance

A martaninsa a karon farko da kamfanin ya yi tun bayan da hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kai samame hedikwatarsa da ke Legas a makon da ya gabata, kamfanin Dangote ya tabbatar da cewa hukumar ta samu wasu takardun da za su taimakawa bincikensu.

Kamfanin ya kara da cewa, ya mika wasu takardu a ranar 4 ga watan Janairu kamar yadda hukumar ta bukata. Sai dai kuma EFCC ta ki amincewa da su, inda ta jaddada cewa jami'anta za su je ofisoshin kamfanin su amsa da kansu.

Sai dai kuma hukumar EFCC ba ta mayar da martani kan sanarwar ta kamfanin ba. Rukunin kamfanin Dangote dai na kasancewa mallakin mutum na biyu mafi arziki a nahiyar Afirka wato Aliko Dangote.