Dakon matatar man Dangote a Najeriya
September 12, 2023Kama daga masu mulki ya zuwa talakawan Tarayyar Najeriyar dai, fara aikin matatar man fetur din Dangoten na zaman babban fatan kawo sauyi wajen wadatar man fetur da kila ma saukinsa. Matatar da ke zaman irinta mafi girma a duniya baki daya an tsara za ta tace gangar mai dubu 650 a kullum, adadin da ya haura daukacin bukatar kasar. Tun a cikin watan Mayu ne dai, aka kaddamar da matatar tare da alkawarin fara aikinta cikin watan Yuli ko Agusta na bana.
Karin Bayani: Najeriya : Martani bayan janye tallafin mai
To sai dai kuma har ya zuwa yanzu babu alamar tace man na Dangote balle sai da shi a Najeriya, abin da ya fara janyo damuwa cikin kasar da ke neman hanyar tunkarar matsalar zare tallafin man fetur din. Dakta Hamisu Yau dai na zaman kwarrare a kan tattalin arziki a Najeriyar, kuma a cewarsa akwai alamun yaudara cikin kasar da ke bukatar sauki. Zare tallafi a cikin karatun gaibu, ko kuma jefa daukacin kasa cikin ni-'yasu dai, kamfanin man kasar na NNPC ne ke da kimanin kaso 20 cikin 100 na mallakin matatar.
Akwai dai fatan fara aikin matatar, ka iya kai wa ga rage farashin man fetur da kila bude sabon babi na rayuwa cikin kasar. Dakta Garba Ibrahim Malumfashi dai na zaman kwararre a fannin makamashi, kuma ya ce ana da kuskure mai girma dangane da dorin fata a kan matatar man ta Dangote. Tarayyar Najeriyar dai ta dauki shekara da shekaru tana tunanin gyara matatun man kasar guda hudu, ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Karin Bayani: Najeriya: Kokarin dakile satar man fetur
Wannan gazawar dai, na nuna alamu na gazawa a bangaren 'yan mulkin da ke tunanin mafita amma kuma ke dada nisa cikin karatun rudu. Injiniya Kailani Mohammed dai na zaman tsohon ma'aikaci a matatar mai da ke Kaduna, kuma ya ce siyasar cikin gida na zaman babbar matsalar da ke sanadin gaza aikin matatun maimakon gazawar hukumomin kasar. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin da ta kaya cikin kasar da al'ummarta ke neman sauki daga radadin zare tallafi, amma kuma ba su da amsar wuju-wuju ina Gabas.