Najeriya: Twitter za ta ci gaba da aiki
January 13, 2022Gwamnatin dai ta bayyana cewa, kafar sadarwar ta Twitter ta cika dukkanin sharuddan da Najeriyar ta gindaya mata. Sanar da dage haramcin da gwamnatin Najeriyar ta yi a kan dandalin sada zumuntar na Tiwitter, na zuwa ne bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu. Matakin gwamnatin ya kawo karshen dogon jira na tsamani da 'yan Najeriya suka yi na tsawon sama da watanni bakwai. Shugaban hukumar bunkasa harkokin sadarwar Internet ta Najeriya Kashifu Abdullahi ne ya sanar da dage takunkumin ga kamfanin na Twitter, cikin wata sanarwa da ya aike ga manema labarai. Tuni aka fara mayar da martani a kan lamarin. A ranar biyar ga watan Yuni na shakarar da ta gabata ta 2021 ne dai gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter daga aiki a kasar, bayan da ta goge wani sako da shafin Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa baya ga zargin kafar da katsalanda da ma tunzura 'yan Najeriya.