1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bamirkiya ta biyo matshi Najeriya

Nasir Salisu Zango LMJ
January 21, 2020

Wata Baturiyar Amirka ta biyo wani matashi dan garin Panshekara a jihar Kano, har gidansu bayan kulla abota a dandalin Instagram, abin da ya kara fito da tasirin Social Media a duniya.

https://p.dw.com/p/3Wc1o
USA Kano Nigeria Social Media Heirat
Ango dan Najeriya da amaryarsa Ba'amurkiya da suka hadu a InstagramHoto: Nasir Salisu Zango

Shekara guda kenan Suleman Isah da aka fi sani da Baba Yaro ya hadu da kawarsa Jenine Sanchez a dandalin sada zumunta na Instagram, a hankali kuma abotar ta zama soyayya me karfi har takai ta biyo shi gidansu da ke Panshekara a jihar Kano. Yanzu haka dai bayan isowar Ba'amirkiyar Najeriya, sun gama cimma yarjejniyar yin aure a watan Maris me zuwa. Tuni dai mahaifiyar Suelaman mai suna Fatima ta ce taji ta gani ta kuma amince da auren amma mahaifinsa Alhaji Isah ya ce yana da hanzari domin sai ya shigar da jami'an tsaro kafin tabbatar da kulla wannan aure. Sai dai duk da haka Suleman da Jenine sun ce babu abin da zai hana su kulla wannan aure.

Tazuarar shekaru tsakanin ma'aurata

Shekarun amarya Jenine dai 46 shi kuma Suleman ango shekarunsa 23 kacal, saboda haka wasu ke sukar auren a kan dalilin bambancin shekaru, dai dai Suleman ya ce ai yin hakan ma koyi ne da sunnar ma'aiki. Ana ta bangaren Jenine Sanchez wacce ta taba yin aure har ma tana da 'ya'ya biyu, ta ce ta shirya tsaf domin auran sahibin nata Suleman ta kuma sa shi a gaba su wuce Amirka, har ma take cewar ta gamsu da yadda suka hadu a Social Media.

Instagram App Logo
Aure sanadin InstagramHoto: picture-alliance/AP Photo/D. Dovarganes

"Hanya ce mai kyau ta haduwa da mutane, kuma ni kam ta yi min daidai dan haka godiya ga Social Media. Na ganshi kuma ya yi min sosai mun yi wa juna daidai, na gamsu za kuma mu yi auranmu a watan Maris."

Social Media: Ci-gaba ko akasin haka?

Batun auren Suleman da Baturiyar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tafka muhawara kan kafofin sada zumuntar na zamani da ake kira da Social Media, wadanda ke kara mayar da duniya tamkar kauye guda. Sai dai akwai tababa kan abin da ya fi rinjaye tsakanin ci-gaban da kafofin sada zumuntar na zamani suka kawo da kuma koma bayan da matsalolin da amfani dasu ke haddasawa. Matasa a jihar Kanon da ma arewacin Najeriyar dai, na da mabambantan ra'ayoyi kan wannan aure na Suleman da Ba'amirkiyar da ta biyo shi har gida. Tuni ma dai Hukumar Hisbah ta jihar Kanon da ma Hukumar Tsaro ta gayyaci Suleman da amaryarsa Jenine domin tabbatar da an shigar da hukumomin da suka dace kafin yin auren da zai kai su ga shillawa jihar Carlifonia ta kasar Amirka.