Bukatar rage Masallatai a Kano
September 7, 2021Malaman na jihar Kano da ke Najeriya dai sun yi wannan kiran ne, a wani mataki na takaita matsalar rarrabuwar kai da ke neman kawo barazana ga addinin Musulumci da Musulmi a jihar. Matakin dai ya jawo korafe-korafe daga masana da sauran jama'a, inda wasu ke ganin hakan a matsayin wani yunkuri na dakile kaifin addini a jihar da ake ganin ta yi shura a fannin addinin Musulunci a duniya. Kiran na malaman ya zo ne bayan taron wuni biyu da Majalisar Malaman Jihar Kanon ta yi, tare da hadin gwiwar jami'ar Bayero da ke Kanon. Manyan malamai da ke wakilcin kungiyoyin addini a jihar da dama ne suka halarci taron, wanda aka fitar da matsaya a fannoni dabam-dabam.
Farfesa Babangida shi ne sakataren majalisar kuma shi ne ya isar da sakon, inda a ciki yake bayyana takaicin majalisar kan yadda wasu cikinsu suka dade da zama 'yan amshin shata wajen zubar da girmansu a gaban 'yan siyasa suna zubewa da yi musu bambadanci dan samun abin duniya. Kunshin matsayar malaman dai ta jawo kace-nace musamman ma batun shawarar rage Masallatai. inda har ma masu fashin baki kamar Abubakar Ibrahim ke ganin cewar wannan dai zance ne kawai da bai dace a jiyo shi daga malaman Kano ba. To amma ga Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale limamin Masallacin Jumma'a na Ihya'ussunah da ke gwammaja, ya ce wannan mataki shi ne daidai domin dama Musulumci ya yi hani da yawan bude Masallatan Jumma'a barkatai sai dai in akwai wani dalili kwakkwara.
Maganar Liman Babangwale ta yi daidai da ra'ayin Farfesa Sani Lawal Malumfashi masanin zamantakewar dan Adam a jami'ar Bayero da ke Kanon, wanda ya ce da ma can malamai ne ke kirkirar Masallatai domin tara magoya baya da sunan neman abin duniya, dan haka matakin kayyadewar yana kan turba. Amma fa a iya cewar an ki a yaba an koma na yaba, domin malaman ne da kansu suka fara karya dokar kiyaye gina Masallatai musamman na Jumma'a. A baya dai sai da izinin masarauta ake gina Masallacin, kafin daga bisani aka sami wasu daga Malamai suka yi wa waccan kai'dar bore.