Karancin ruwan sha a Kano da kewaye
June 25, 2024Duk da ana samun ruwaa wasu yankunan birnin Kano jefi-jefi, amma a wasu an dade ko da digo guda ba ya zuwa musu. Malam Magaji Sani Garba mai nama Jakara cewa ya yi tuni suka hakura da ruwan famfo: ''A kalla shekara tara rabonmu da ruwan famfo don gaba daya ma ba ya zuwa idan dai daga Goron Dutse ne abin da ya yiwo Chediya,Jakara, Muskwani zuwa nan Makera ‘Yan Doya ke nan babu maganar ruwan famfo sai dai mu nema mu saya:'' Shi kuwa Malam Bashir Yahya Umar Chediyar ‘Yan Gurasa koka wa ya yi da yadda tsadar ruwa ta shiga jerin kayan masarufi da tsadarsu ta sha musu kai: ''Magana da gaskiyya ruwa muna cikin matsalarsa, fiye da inda ba a zato.Ana sayen ruwa Naira dari duk jarka daya. Shi ya sa talaka yake a cikin wani hali domin yanzu bayan tunanin maganar sayen abinci, ruwa ma sai an sa shi a lissafi a gida. Don haka maganar saukin samun ruwa, an sami sauki ta dalilin idan ruwan sama ya sauka.
Gargadin hukukomin kiwon lafiya game da yin amfani da ruwan sama
A yayin da ruwan saman ke zamewa mutane da dama mafuta ta wahalar ruwa da suke sha, shi kuma kwamishinan lafiyar Kano gargadi ya yi ga jama'a da su guji amfani da ruwan sama kai tsaye. Ga dai ra'ayin Magaji kan hakan. ''Gaskiya dai a cikin gari matsalar yadda ake bukatar ruwa, gaskiyya ba abu ne mai yiwu wa ba, ka tari ruwan saman kana kallonsa mai kyau garai-garau kuma ka kasa sha.Gaskiya ba abu ne mai yiwuwa ba a cikin gari amma zai iya yiwu wa a wani bangaren amma dai ba a nan yankin ba.