Kano: Abba Kabir Yusuf ya sha kaye a Kotu
October 2, 2019Lauyoyin jam'iyar PDP da Abba Kabir Yusif da ya yi takarar gwamnan Kano a karkashinta, sun bayyana rashin gamsuwa da hukuncin kotun sauraron karar zaben gwamna wacce tayi fatali da korafin da suka shigar na kalubalantar nasarar Gwamna Ganduje a matsayin gwamnan Kano.
Tuni dai mabiya darikar Gandujiyya suka shiga murna yayin da hukuncin ya zama tamkar abin jimami ga daukacin mabiya tafarkin Kwankwasiyya a Kano
Alkali Halima Shamaki shugabar kotun saurar karar zaben gwamnan Kano ce ta karanta hukuncin da ya tabbatar da nasarar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
Wannan hukunci dai bai yiwa 'yan jamiyyar PDP masu bin tafarkin kwankwasiyya dadi ba, har ma lauyoyin jam'iyyar ke cewar sun shirya tsaf domin garzayawa kotun daukaka kara da nufin kalubalantar wnanan hukunci wanda suka ce an yi shi ne da nufak.
Bashir shi ne lauyan da ya yi magana a madadin lauyoyin PDP da dan takararsu Abba Kabir Yusuf, ya ce kotu ta fadi ra'ayinta, amma basu gamsu ba don haka zasu kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara dama kuma ba wannan ne farau ba da suka kalubalanci ra'ayin wannnan kotu aka je gaba kotun sama ta yi fatali da ra'ayin kotun dan haka ya ce yakin dai yanzu aka fara.
To amma ta Bahaushe da kan ce yayin da wani ke kuka da tagumi, wani kuwa lokacin yake shewa da murna domin a nasu bangaren lauyoyin jam'iyyar APC da gwamna Ganduje sun ce kotu tayi adalci kuma an dora kwarya akan bigiren da ya dace dan haka suke cewar koda ma an je kotun daukaka karar ba za ta sauya zani ba.
Barista Ibrahim Muktar shine tsohon kwamishinan sharia na jihar Kano kuma wanda yayi Magana a madadin lauyoyin jamiyyar APC da gwamna Ganduje yace PDP tayi daawa kuma ta kasa kare da awar,
Barista Abba Hikima Fagge lauya ne mai zaman kansa a Kano, ya bayyana cewar jam'iyyar PDP tana da hujjojin samun nasarar wannan sharia, sai dai an sami akasi wajen gabatar da hujjojin a gaban kotun shi ne ma ummul aba'isin da yasa suka karci kasa a gaban a ya yin shariar.
Sukuwa mutanen gari a nasu bangaren, an sami kaulani inda wasu ke cewar sambarka madallah da Ganduje wasu kuma masu biyayya ga tafarkin kwanakwasiyya ke gurnani tare da mararin sauraron abin da zai kaya a kotun daukaka kara.