1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Karfin ikon shugaban Amurka karkashin tsarin mulki

January 20, 2025

Donald Trump na shirin aiwatar da wasu manyan sauye sauye a Amurka a shekaru hudu masu zuwa na wa'adin mulkinsa na biyu. Ikon zartar da doka ta musamman ta shugaban kasa zai kasance hanyar da zai aiwatar da wannan kudiri

https://p.dw.com/p/4pORG
Trump ya yi rantsuwar kama aiki
Trump ya yi rantsuwar kama aikiHoto: Julia Demaree Nikhinson/AP/dpa/picture alliance

Kundin tsarin Amurka ya bai wa shugaban kasa karfin iko na gudanar da wasu dokoki da zarar an rantsar da shi kan karagar mulki ba tare da sahalewar majalisar dokokin kasar ba. Shugaban Amurka na 47 Donald Trump ya bi sahun magabatansa wajen kafa tarihi na aiwatar da dokar da ake yi wa lakabi da Executive Order.

Donald John Trump ba shi ba ne shugaban Amurka na farko da ya aiwatar da dokar gaggawa a ranar da ake rantsar da shi ba, hasali ma tsohon shugaban kasar Joe Biden ya rattaba hannu kan dokoki guda tara a ranar da aka rantsar da shi, wadanda haunin biron Trump za su yi awon gaba da wasu dokokin musamman yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi.

Karin Bayani: Scholz na Jamus ya jaddada aniyar aiki da Trump na Amurka

Biden da Trump wajen rantsar da shugaban kasa a majalisar dokoki
Biden da Trump wajen rantsar da shugaban kasa a majalisar dokokiHoto: Melina Mara/AFP

To sai dai a wannan rana ta Litinin an yi wasa da jan biro wajen rattaba hannu kan dokokin da shugaban ke da karfin iko, ciki kuwa har da batun afuwa ga tsagerun mutanen nan masu fushi da fushin wani da suka kai wa ginin majalisar dokokin kasar ta Capitol Hill hari a ranar 6 ga watan Janairu 2021.

Rattaba hannu kan wadannan dokoki ka iya bude sabon babin siyasa a duniya da kuma alkiblar siyasar Amurka a gwamnatin shugaban Amurkan na 47. To amma wace doka ce ta samar da wannan karfin iko ga shugaban kasa a Amurka kuma shin hakan zai ci karo da dokokin kasar? Bert Rockman, malami ne a sashen koyar da kimiyyar siyasa a Jami'ar Purdue da ke Amurka ya ce dokar na da dadadden tarihi duk da cewa Trump zai fuskanci shari'u da dama daga masu sukar manufofinsa.

Karin Bayani:Shugaba Trump zai shata makomar TikTok a Amurka

Taron rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa
Taron rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasaHoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

"Babu makawa za a samu sabanin fahimta dangane da aiwatar da wadannan dokoki tsakanin bangaren zartarwa da fannin shari'a, har ma da majalisar dokoki; dole ne za a samu rashin fahimtar juna dangane da wadannan dokoki”

Shin akwai iyaka dangane da adadin dokokin da ya kamata shugaba ya rattaba wa  hannu? A kundin tsarin mulkin kasar dai babu, alal misali shugaba Franklin D. Roosevelt ya rattaba hannu kan irin wadannan dokoki na Executive Order sau 3,721 kuma mafi yawa ke nan a tarihin Amurka. Mr. Rockman na Jami'ar Purdue, ya ce dokoki kalilan ne za su yi tasiri daga cikin 100 da Trump ya ke so ya aiwatar.

"Haka ne zai iya rattaba hannu kan dokoki sama da 100, duk da cewa galibinsu basu da wata matsala, to amma akwai wadanda sai an kai ruwa rana wajen aiwatar da su kamar batun dokar bakin haure da kuma wadda ta shafi fasalta tsarin gudanar da aiki a hukumomin gwamnati duk da cewa ba nan take za a aiwatar da dokokin ba.

Karin Bayani:Trump ya yi barazanar kara haraji kan EU

Rantsar da Donald Trump
Rantsar da Donald TrumpHoto: Kenny Holston/The New York Times/AP/picture alliance

Mitch Sollenberger, na Jami'ar Michigan-Dearborn  a Amurka ya ce Trump zai fara karin kumallo da shari'u a kotunan kasar a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Idan muka yi waiwaye kan dokar da Trump ya rattaba hannu a 2017 kan haramta wa baki daga wasu kasashen musulmi shiga Amurka, kungiyoyin musulmi da masu rajin kare hakkin ‘dan Adam sun gurfanar da shi a gaban kotu wanda har aka dangana da kotun kolin kasar da kungiyoyin musulmin ne suka yi nasara.

Wasu daga cikin dokokin da Trump zai rattaba hannu a kai sun hadar da sake fice wa daga yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO har ma da dokokin da suka shafi diflomasiyyar Amurka da kasashen ketare.