Najeriya: Karuwar hako gangar man fetur
January 7, 2025Tarayyar Najeriyar dai, na fafutukar rage yawan cin bashi da ma biyan wanda ake bin ta a yanzu. Kaso kusan 40 cikin 100 na daukacin kudin da Tarayyar Najeriyar take shirin ta batar a shekarar bana dai, na shirin fitowa daga jerin basussuka ba adadi. Ga kasar da tace tana shirin cin bashin da ya kai kusan triliyan 14 na Naira ta kasar, kafin iya aiwatar da sabon kasafin kudi na shekarar bana. To sai dai kuma mahukuntan Najeriyar sunce suna hango haske cikin batun kudin, tare da samun karin yawan man fetur na sayarwa a kasashen ketare. Najeriyar a karon farko a shekaru kusan hudu, ta ce ta share tsawon watan jiya tana hakar gangar mai miliyan daya da dubu 500, adadi mafi yawa cikin kasar da ta dauki lokaci tana gwa-gwa-gwa da barayin man da ke a yankin Niger Delta. Sabon adadin dai daga dukkan alamu na zaman sabon fata ga masu mulki na kasar da ke fadin suna bukatar girma, amma kuma ke dada nisa a cikin kogin bashi. Abdulaziz Abdulaziz dai na zaman daya a cikin kakaki na gwamnatin tarayyar, da kuma ya ce sabon karin na nufin kara yawan kudin shiga da ma rage bashin da ke ta tarnaki ta fannoni da yawa.
Koma wane tasiri sabon adadin yake shirin yayi ga kokarin kasar na rage dogaro a kogin bashin dai, daga dukkan alamu tana da babban aiki na burge 'yan kasar da ke fadin da sauran sake. An dai dauki shekara da shekaru ana nunin yatsa, cikin kasar da hajjar man fetur ke zaman kafar wadaka da kila ma biya na bukatu na kalilan da ke madafun iko. Sabo Imam Gashuwa dai na zaman mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP reshen Arewa maso Gabashin kasar, 'yan kasar ba sa gani a kasa daga karuwar arzikin man fetur din a halin yanzu. Tasirin arziki ga rayuwa da makoma ko kuma wadaka da dukiyar al'umma, a shekara ta 2023 ne OPEC ta rage yawan kason man fetur din Najeriyar daga ganga miliyan daya da dubu 800 zuwa ganga miliyan daya da dubu 500. To sai dai kuma Abujar tana da bukatar sauyin taku bisa hanyoyi na arziki kafin iya kaucewa bashin, a tunanin Dakta Isa Abdullahi da ke zaman kwarrare ga tattalin arzikin kasar. Tun daga shekarun 1970 da kasar take fadin ta kai karfi, ana ta'allaka koma-bayan tattalin arzikin Najeriya da dogaro a kaco-kam bisa hajjar man fetur din da ta kai kasar zuwa mafarkin rana amma kuma ke neman mai da ita zuwa bara da neman bashi.