Cudanya tsakanin likitocin Masar da Najeriya
May 24, 2019Talla
Musanya ta dalibai daga jami'o'i a fannin kiwon lafiya daga wata jami'a zuwa wata jami'ar don karin ilimi ya kan taimaka sosai wajen samun kwarewa da kuma kara fahimta a daidai lokacin da sabbin na'urori na kula da sha'anin kiwon lafiya ke kara bazuwa a duniya. Wannan yarjejeniya da jami'o'in biyu suka kulla za ta bai wa daliban kasashen damar daukar ilimi a Najeriya da Masar, abin da zai taimaka wajen kawo ci-gaba ga sha'anin kiwon lafiya a kasashen biyu.