Karshen zaman dirshen kin jinin sojojin Faransa a Nijar
December 29, 2023Firaministocin Burkina Faso da Mali da Nijar sun kasance manyan baki a harabar barakin sojojin sama na birnin Yamai, isansanin da 'yan fafutukar kawar da sojojin Faransa daga kasar Nijar suka kwashe watanni hudu suna zaman dirshen har sai sojojin Faransa sun fice daga kasar ta Nijar. Firamnistocin karkashin kungiyar kawance ta kasashen Sahel AES sun jinjinawa alummar kasar kan jajircewar da suka yi duk kuwa da takunkumi da ke ci gaba da kawo cikas ga harkokin yau da kullum.
Karin Bayani: Tiani ya juya wa yarjejeniyoyin tsaro da waje baya
Dandalin ya cika makil da magoya bayan juyin mulki da masu fafutukar kyamar sojojin Faransa, sai dai a yayin da suka iso wurin wannan babban taro firaministocin ba su yi wata magana ba, sun hau mumbarin taron inda suka daga hannuwa domin gaisuwa ga jama’a kafin su fice cikin gari domin ganawa da magabatan kasar ta Nijar.
Karin Bayani: Takun saka da kungiyar kasashe rainon Faransa
Malumai na daga cikin wadanda suka kasance a sahun gaba wajen wannan gwagwarmayar ta kyamar Faransa, inda suka taka rawar gani sosai wajen fadakarwa ta hanyar wa’azi da addu’o’i don ganin Nijar ta kwana lafiya ta tashi lafiya tare da samun hadin kan yan kasa baki daya. Daga cikin wadanda suka taka rawar gani wajen wannan kokowar ta kyamar sojojin Faransa, akwai jami'an sa kai "brigade de veille" masu sa idanu a dukannin mayan shatale-tale na birnin Yamai domin kama wa jami’an tsaro a fannin tsaro tun bayan da ECOWAS ta yi shelar daukar matakan soji a Jamhuriyar Nijar.
Karin Bayani: Iyalan Bazoum sun maka talabijin RTN a kotu
A yanzu kungiyoyin fararen hular da suka yi wannan fafutukar sun bayyana manufarsu ta karkata kokawar zuwa ga yaki da wadanda suka yi wa tattalin arzikin Nijar zagon kasa.