Tiani ya juya wa yarjejeniyoyin tsaro da waje baya
December 27, 2023
Tun bayan hawan mulkin hukumar soja a ranar 26 ga watan Yuli ne, sojojin da 'yan kasa masu mara musu baya suka jajirce wajen tabbatar da cikaken 'yancin kasar ta hanyar kare muradunta ta kowane bangare. Wannan ne ya sa gwamnatin ta Nijarta hanyar ofishin ministan harkokin wajen kasar ta sanar wa dukkannin kasashen da ke da rundunar sojoji da aka jibge a yankunan kasar, cewa Nijar za ta gudanar da nazari kan dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla da su domin sabunta su. Ko da Farfessa Dicko Abdourahamane, malami a jami'ar Andre Salifou da ke birnin Damagaram sai da ya ce dole ne a yi waiwaye adon tafiya kan yarjejeniyoyin tsaro.
Karin bayani:Tiani ya gode wa 'yan Nijar da suka ba da tallafi
Masu sharhi kan harkokin tsaro a yankin Sahelirin su Malam Kabirou Issa na ganin cewar yin hakan tamkar wata dama ce ta samun yarda da juna tsakanin wadannan kasashen waje da sojojinsu suka rage a kasar ta Nijar. Su kuwa 'yan siyasa irin Soumaila Amadou, wanda ke bin abubuwan da ke wakana a kasar ta Nijar sau da kafa yana kuma ba da ra'ayoyi ta shafukan sada zumunta na ganin cewa ba dukkan sojojin kasashen waje ne ke zaune a Nijar da niyyar cuta ba.
Karin bayaniPistorius na neman karfafa huldar tsaro da Nijar:
Sai dai a cewar Atto Namaiwa, masanin dokokin shari'a kuma malami a jami'ar birnin Tahoua ya kamata doka ta ba da izinin sake duba yarjejeniyoyi, amma kuma ba wannan mataki ne 'yan kasar ta Nijar ke jira daga sojojin da ke mulki ba.