1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar barazana daga Boko Haram

August 25, 2014

Hankulan al'ummar Tarayyar Najeriya na kara tashi sakamakon karuwar barazana daga kungiyar Boko Haram bayan da ta ayyana kafa daular Musulunci a garin Gwoza.

https://p.dw.com/p/1D0zZ
Hoto: imago/Wolf P. Prange

A Abuja babban birnin kasar hankula na kara tashi ga 'yan siyasa dama shugabannin da ke kallon karuwar barazana mafi girma ga yakin ta'addancin kasar dake cikin shekarar sa ta biyar. A can kuwa yankin arewa maso gabashin kasar da ke cikin dokar ta baci ana gwabza fada a tsakanin sojojin kasar da ke kokarin kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram da kuma 'ya'yan kungiyar da daga dukkan alamu ke kokarin kara fadada sabuwar daular da suke fadin sun kai ga kafawa.

Babu dai zato ba kuma tsammani shugaban kasar ya kai ga katse wata ziyarar neman lafiyar da ta kai shi kasar Jamus ya kuma iso birnin Tarayyar na Abuja domin nazarin barazanar da ta kai ga aiyana wasu sassan kasar da yake mulki a matsayin sabuwar daular kungiyar mai kara tasiri.

Duk da cewar dai sai ya zuwa Talatar nan ne ake zaton yin wani taron majalisar tsaron kasar dake da ruwa da tsaki da kokarin nasarar yakin dai, daga dukkan alamu 'ya'yan majalisar na shirin tunkarar kalubalen fidda wando ta tsakar ka ga sojan kasar da alamu ke nuni da cewa ruwan yakin na neman wucewa da sanin karfinsu.

Boko Haram ta kwace garuruwa

Kama daga Madagali ya zuwa Marte da uwa uba Gwoza da ke zaman cibiyar sabuwar Daular, kama da wutar daji ne dai sabuwar daular ke kara girma dama tasiri a fadar Senata Ahmed Zanna da ke wakiltar Borno ta arewa maso gabas a majalisar dattawan kasar ta Najeriya da kuma ya kai ga asarar wasu bangarorin nasa ga 'yan kungiyar a halin yanzu.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar ShekauHoto: picture alliance/AP Photo

" Ba Gwoza da Madagali bane kadai ke hannunsu Damboa ma har yanzu na hannunsu, Marte na hannunsu, yau kuma anje Gamboru Ngala yanzu haka sune suke yawo a cikin gari sojojin na nan a bakin gada babu ko daya a cikin gari. Saboda haka maganar Gwoza da Madagali ba haka bane ga Buni yadi ga Gwonori duk gaba daya na hannunsu, kuma in ka bar Maiduguri in ba Mafa da Bama da Konduga ba kowannensu in ka fita Kilomita biyu yaran nan suna nan suna yawo da baburansu da motocinsu.”

Rahotannin dake fitowa daga Kamaru ma dai na nuni da tserewar sojojin Najeriyar kusan 480 ya zuwa cikin kasar da nufin kaucewa fadan da suke ta'allaka kauce masa da rashin isassu na kayan yaki dama hadin baki na shugabanninsu.

A cikin watan Yunin da ya wuce ne dai majalisun dokokin kasar biyu suka kai ga amincewa shugaban kasar ya sake tsawaita dokar ta-bacin da ta baiwa sojan ikon yin gaban kansu cikin yankin a bisa sharadin nazarin ta a duk tsawon wata wata. Nazarin kuma da ya sha ruwa a bangaren 'ya'yan majalisar da sukai kunnen uwar shegu da annobar daga dukkan alamu kuma suke shirin ganin ba dadi ya zuwa yau din nan. Abun kuma da a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban cibiyar Cislac mai kula da aiyyukan 'yan dokar kasar ta Najeriya ke kara fitowa fili da alamu na gazawa a bangarorin biyu da ke ikirarin mulkar kasar a halin yanzu.

Nigeria Soldaten
Sojojin Najeriya a jihohin da ke karkashin dokar ta baciHoto: AFP/Getty Images

Ra'ayin kungiyoyin farar hula

“Tun da ana samun wannan barkewar rashin kwanciyar hankali ya dace ace sun dawo sunyi nazari a kan rahoton nasara ko rashin ta. Majalisa ba ta kira domin nazarin ci gaba ko rashin ci gaban dokar ba kamar yadda aka tsara, kaga alama ce ta rauni ga shugabancin da ke tafiya a majalisar”

Kokari na ayyana daular dai daga dukkan alamu na zaman kalubale mafi girma ga mahukuntan kasar da suke fadin sun kusan isa gaci amma kuma har yanzu ke nuna alamar kasawa a cikin rikicin. Abun kuma da yanzu haka ya fara dora ayar tambaya bisa tasirin dokar tabacin kasar da daga dukkan alamu ke kara batawa maimakon gyara makomar al'ummar yankin a fadar Senata Zannan da ya ce kokarin neman sake zaman majalisar da ke wani hutu na karshen shekara yaci tura a bangarensa.

"Na nemi in ga shugaban majalisar dattawa amma har yanzu bai yiwu ba, amma dai ina iyakar kokari na na ganin an sake kiran zaman majalisa domin nazarin abun da ke akwai. Tun da farko mu munyi adawa da dokar tabacin amma shugaban mu yace a wannan karo zai tabbatar da ganin duk abun da ya kamata sojojin suyi sunyi don ganin nasarar dokar in ba haka ba to komai yana kansa"

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba da fadar gwamnatin kasar da shugabanta ke kartar kasa ta siyasa dama 'yan majalisun da ke neman sake zuwa a dama dasu na ganin karshen rikicin da nufin burge al'ummar yankin dama arewacin kasar ta Najeriya zasu dauka.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ AH