1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Najeriya: Yaki da zazzabin cizon sauro

December 7, 2021

Kasa da shekaru hudu da cimma wa'adin kawo karshen zazzabin cizon sauro a cikin Tarayyar Najeriya, daga dukkan alamu har yanzu tana kasa tana dabo cikin kasar da cutar ke kara yaduwar tsakanin al'ummarta.

https://p.dw.com/p/43xed
Anopheles Mücke
Zazzabin cizon sauro na ci gaba da yin illa a NajeriyaHoto: David Spears/Ardea/imago images

Babban burin Tarayyar Najeriya dai, na zaman kai karshen cutar zabbabin cizon sauron nan da shekaru hudun da ke tafe. To sai dai kuma ga dukkan alamu tana shiga dawa ga karuwa ta yaduwar cizon sauron, ga kasar da ta darma sa'a wajen yawa na masu dauke da cutar. Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na shekarar bana, ya ce Najeriyar ce ta ciri tutar zama ta kan gaba a duniya ga yawan mutuwa daga zabbabin mai zafi. Sauron dai a fadar rahoton na bana ya halaka mutane sama da dubu 150 a cikin Najeriyar, ko bayan yara 'yan kasa da shekaru biyar miliyan 13 da suka karbi maganin neman waraka daga cutar.

Karin Bayani: Sabon tsarin yakar zazzabin cizon sauro a Nijar

To sai dai kuma duk da kasancewar sauron na kan gaba wajen kisan yaran da ke da kasa da shekaru biyar a Najeriyar dai, hankalin 'yan mulki na kasar ya fi karkata zuwa ga corona, cutar da ta kashe kasa da mutane 3,000 cikin kusan shekaru biyu. Kimanin Naira miliyan dubu 400 ne dai Najeriyar ta ware domin tunkarar annobar covid19, a yayin da kusan mafi yawa na Naira miliyan dubu 120 da ake kashewa ga maganin na zazzabin cizon sauron ke fitowa daga aljihun talakawa.

A cewar Dakta Umar Tanko da ke zaman wani likita mai zaman kansa a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar akwai wahala kafin a iya shawo kan matsalar da ta zama tarihi a kasashe na duniya da daman gaske. Sama da mutane miliyan 60 ne dai suka kai ga kamuwa da cutar ta zazzabin cizon sauron, kuma mafi yawansu na zaune a kauyukan da ba su da isassun cibiyoyin lafiya a cikinsu. Ko bayan gaza samar da magani na hukuma dai, da dama cikin 'yan kasar ba su da damar kai wa ga dakunan gwajin da ke tasiri a kokari na tabbatar da kamuwa da cutar balle su samu magani mai tasiri.

Karin Bayani: Me ke sa cuta ke bijire wa magani?

To sai dai kuma a fadar Garba Umar Pella tsohon jami'i a kungiyar Roll Back Malaria da ke jagorantar neman rage karfin cutar, sauya hali na iya tasiri a cikin neman raba Najeriyar da illar sauro. Babban fata ga kasar dai na zaman wani sabon tsarin riga-kafin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce na iya tasiri ga kokarin kare mutuwar yaran da ta kai kusan dubu 260 a kasashen da ke Kudu da Hamada ta Sahara.