Ghana: Kalubalen sabon jadawalin karatu
August 6, 2024Gwamnati dai ba ta nuna ko alamar ranar fitar da littattafan ba, ko kuma yin wani bayani a kan al'amarin da ya sanya dalibai ke fama a wajen nazari. Gwamnatin Ghana dai, na rage dadin kudin da ake bukata na samar da ilimin yara a kullum. A shekara ta 2019 gwamnati ta sanar da fitar da sabon jadawalin karatu daga matakin sharar fage har zuwa aji shida na makarantun frimare. An dai ta bayyana jerin kalubale a lokacin, wanda har yanzu daya cikinsu na ci gaba da kawo nakasu ga sha'anin ilimin. A makarantun gwamnati dai, a kan samu yara hudu zuwa biyar na amfani da littafi guda daya, kuma a hakan ma daliban ne suka kawo da kansu ko kuma iyayensu ne suka siya.
A shekaru biyun da suka shude, ma'aikatar ilimi ta bai wa masu kwangilar buga littattafai wa'adin ranaku 120 su kammala buga wa a rarraba ga yara. Ministan ilimi ya yi tattakin bin sahunsu, daga bisani ya bayar da tabbacin samar da littattafan kafin watan Satumba na shekarar 2021. Sai dai haka ba ta cimma ruwa ba, kasancewar kadan da aka samu ba su isa a raba su ga kowa ba. Al'amarin na da sarkakiya domin a makarantun firamare dalibai ke siyen kayan makaranta da littattafai sabanin a makarantun sakandire, inda da alama manufar siyasa ta yi tasiri tare da haifar da tambayoyi da dama wanda mafi karfi ita ce ko shin makarantun firamare da bukatunsu ba su da muhimmanci ne?