1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kudin Jamus ya karu saboda yakin Ukraine

Sabine Kinkartz AT Bala
March 25, 2022

Jamus ta tara sabbin bashi na biliyoyin Euro kamar yadda tsarin kasafin kudin 2021 da 2022 suka nunar. To amma abin bai tsaya a nan ba. Yakin da ake yi a Ukraine ya sa kudaden na dada karuwa.

https://p.dw.com/p/493gG
Deutschland | Bundestag Infektionsschutzgesetz
Hoto: Michele Tantussi/REUTERS

A kasafin kudin gwamnatin na shekarar 2022 an tsara Jamus za ta kashe kimanin Euro biliyan 23 wajen gudunmawar jinkai wannan adadi ya yi daidai da digo bakwai cikin dari na abin da kasar za ta kashe.Sai dai kuma kasafin kudin ma'aikatar raya kasa wanda ya hada da kason taimakon jinkai zai ragu da fiye da kashi 12 cikin dari wato euro biliyan goma da miliyan dari takwas. A muhawarar da aka yi majalisa shugaban gwamnati Olaf Schulz bai boye komai ba wajen baiyana cewa kudin ba za su isa ba, wannan kuwa tun ma kafin yakin Ukraine kenan a saboda haka kalubalen suna da yawa.Ba kasafai wani wakili na gwamnati yake kalelaice kasafi kamar yadda Svenja Schulze ministar tattalin arziki da raya kasa ta yi ba a farkon fara muhawara kan kasafin kudin a majalisar dokoki ta Bundestag:Ya ce. '''Yakin da ke gudana a yankin da aka fi samar da abinci a duniya yana yin mummunan tasiri akan wadatar abinci a duniya baki daya: Farashin abincin tuni ya yi tashin gwauron zabi a kasuwanni wanda aka dade ba a gani ba tun shekarar 2008. Duk kwana daya da aka kara a wannan yaki hasarar rayuka ake yi da kuma yunwa. Shi ya sa ya zama wajibi mu yi duk bakin iyawar mu ga kare aukuwar annobar yunwa."

Jamus ta kara yawan kudaden da take kashewa a kasafin kudi na shekara

Deutschland | Bundestag Infektionsschutzgesetz
Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

Wani abu da ba a tsinkaye shi ba a cikin kasafin kudin shi ne kudin da mamayen da Rasha ta yiwa Ukraine zai jawo wa Jamus. Kasafin bai yi la'akari da tasirinsa ba da kuma karuwar farashin makamashi ko kuma kai komon da zai biyo bayan takunkumin da aka kakaba wa Rasha. Kudin da za a kashe wajen taimakon jinkai na iya kasancewa cikin alkaluman da aka bayar amma kudin da za taimaka wa mutanen da ke gudun hijira daga Ukraine zuwa Jamus ba a sanya shi a cikin kasafin kudin ba.Ma'aikatar tattalin arzikin ta ce a yanzu ba zai yiwu a iya yin kiyasin ko ya dace a ciwo wani bashi ba kuma idan zan a yi nawa ya kamata a ciwo? Ma'aikatar dai ta tsara gundarin kasafin kudin da majalisar zartarwa za ta amince da shi kafin a tura wa majalisar dokoki domin amincewarta wanda ya tasamma euro miliyan dubu 457 da miliyan dari shidda.Sai dai Hermann Gröhe na jam'iyyar CDU a majalisar dokokin ya soki lamirin shirin rage kudin taimakon jinkai bisa la'akari da mutane miliyan 800 da ke fama da yunwa a duniya a daidai lokacin da ake bukatar hadin kai a duniya: "Yace a lokacin da ake bukatar hadin kan duniya, kasafin kudin ma'aikatar tattalin arziki da kawancen raya kasa ya ragu da kimanin euro biliyan daya da miliyan dari bakwai. Wannan ya nuna rashin daidaiton tsari a bangaren wannan gwamnatin Shin babu wanda ya lura da hakan? haba wannan ba abin da za a lamunta da shi bane."Tuni kungiyoyin bada agaji karkashin hadaddiyar kungiyar agaji ta Jamus  Venro suka ce za a sami raguwar Euro biliyan 31.2 a kasafin raya kasa da taimakon jinkai wanda suka ce ba zai kai cimma bukatun da ake nema ba da suka hada da yaki da sauyin yanayi da samar da abinci da kuma kiwon lafiya).