290911 Euro-Rettungsschirm Bundestag
September 29, 2011A jimilce 'yan majalisa 523 ne suka kada kuri´ar amincewa a yayin da 85 kacal su ka nuna adawa da wannan mataki.
Baki daya asusun mussamman da kasashenTurai su ka kuduri girkawa domin taimakawa kasar Girka ya kunshi tsabar kudi euro miliyan dubu 440.
Kasar Jamus ta fi bada tallafi mai tsoka tare da euro miliyan dubu 211.
Klauss Peter Willsch dan majalisar dokoki a karkashin tutur jam´iyar CDU mai mulki, to amma ya na daga yan tsirarun yan majalisar CDUn su goma,wanda su ka kada kuri´ar kin amincewa da matakin ceton kasar Girka, kuma ya bada hujjojinsa da cewa:
"Maganar lodawa kasa bashin da ya karfinta ba daidai ne ba.Sannan Jamus za ta ware zunzurutun kudi har euro miliyan dubu 211, kudin wannan ba su ke gare mu ajje ba,kawai bashi ne za mu yi ta lodawa diyanmu da jokokinmu."
To saidai a cewar shugaban Majalisar dokokin Bundestag Norbert Lammert, taimakawa Girka ta fita daga halin da take ciki ya zama wajibi ga kasar Jamus da ke matsayin jagoran kasashen Turai:ya ce wannan kuri´ar amincewa da muka kada na daga cikin mahimman aiyukan tarihi da majalisarmu ta gabatar.Ta la´akari da yadda matsalar ta yi kamari a Girka,cilas babban goro sao magogi na kwarai.
Duk da amincewar da 'yan majalisar Jamus su ka yi na taimakawa Girka, har yanzu ba a gama tattara kudaden da ake bukata ba domin cimma burin da aka sa gaba, inji ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble:Kudaden da muka tanada a cikin Asusun bai daya na taimakon Girka har yanzu da saura.To amma wannan kuri´ar amincewa da Majalisar Dokokin Bundestag ta kada manuniya ce ga sauran kasashen da ya rage wanda mu ke kyautata zaton suma za su bi sahu.
A wannan Alhamis,wakilan murhun rukunnan da suka fi yawan kudin bashi a Girka wato Kungiyar Taraya Turai, Babbar bankin kasashen Turai da Asusun bada lamuni na duniya, sun yada zango a birnin Athena domin tattanawa da magabata game da hanyoyin kubuta daga halin da kasar ta shiga,sannan su duba yiwuwar sake taimaka mata da wani saban bashi na euro miliyan dubu takwas a cikin wata mai kamawa.
Hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayya Turai ta bayyana matukar gamsuwa ga matakin da Jamus ta dauka, kawo yanzu kasashe 11 daga cikin kasashe 17 masu amfani da takardar kudin euro su ka amince da tsarain ceton kasar Girka.A yan kwanaki masu zuwa, sauran majalisun dokokin kasashe shiga wanda su ka hada da Austriya za su kada kuri´a domin bayyana matsayinsu game da fassalin ceton Girka.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman