Martanin kasashen duniya kan harin Isra'ila a Siriya
April 2, 2024Antonio Guterres yi kira da a kaucewa duk wani tashin hankali yana mai gargadin cewa lamarin na iya haifar da rikici a yankin da ba a taba samun kwanciyar hankali ba, tare da mummunan sakamako ga fararen hula.
Iran ta kudirin aniyar mayar da martani kan Isra'ila
Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kazamin harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus da Isra'ila ta kai, harin da ba a taba ganin irinsa ba wanda kasashe da dama suka yi Allah wadai da shi, wanda kuma ke kara tada jijiyoyin wuya a yankin Gabas ta Tsakiya a tsakiyar yakin Gaza. A ranar Litinin makamai masu linzami guda shida da Isra'ila ta harba Siriya sun lalata ginin ofishin jakadancin Iran a Siriya da kuma gidan jakadan Iran, inda suka kashe mutane 13, 'yan Siriya shida da 'yan Iran bakwai, a cewar gidan talabijin na kasar.
Damuwar kasashen duniya a kan harin da yakan iya haddasa tashin hankali a Gabas ta Tsakiya
Kasar China yi Allah wadai da harin wanda ta ce ta karya dokokin tsaro ne da huldar diplomasiya yayin da kungiyar tarayyar Turai ta yi kira ga kamun kai. Shugaban diflomasiyar Iran Hossein Amir-Abdollahianya sanar da cewa, ya aike da sako mai mahimmanci ga Amurka, wanda a matsayinta na masu goyon bayan gwamnatin IOsra'ila dole ne su dauki nauyin abin da zai biyo ba.