'Yan wasan Afirka na ba da himma a gasar Paralympics
September 4, 2024Kasar Tunisiya da Moroko sune kan gaba a kasashen Afirka wajen lashe kyautuka inda suka yi kunnen doki kowacce take da lambobin yabo bakwai. Sai kuma Aljeriya da Afirka ta Kudu da su ma kowacce take da hudu. Ita ma dai Najeriya da ta gaza samun ko da kyauta guda a gasar Olympics da aka kammala a watan Augusta ta samu lashe azurfa da tagulla guda guda, lamarin da ya sa masharhancin lamuran wasanni a Bauchi Yahuza Yahaya Doka ya ce tabbas sun daga kima da martabar Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afirka a duniya yana mai amfani da wannan azancin maganar.
'Nakasa a zuci take ba a fili ba, ni a ra'ayina wadannan sun ma fi sauran bangarorin wasanni duba da halin da ake ciki a Najeriya ba kowa za ka tsare ka samu yana mai da hankali a kan harkar wasanni ba in ba irin wannan ba. Ka ga daidai gwargwado a yanzu dai sai dai mu ce Allah-san-barka hade da kasashenmu na Afirka musamman bangaren masu bukata ta musamman''
Maryam Bolaji daga Najeriya tana daga cikin wadanda suka samu nasara a wasan kwallon Badminton inda ta samu tagulla lamarin da kuma ya faranta ran 'yan kasa masu bibiyar gasar ta Paralympics har ma suke ganin kafin a kai ga kammala gasar akwai yiwuwar Najeriya ta kara samun wasu kyautukan da suka hada da zinare kamar yadda wasu kasashen Afirka suka samu duk da cewa ana ganin sai sun kara kwazo.