1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka ta Yamma na fuskantar yunwa

Binta Aliyu Zurmi
April 5, 2022

Miliyoyin mutane a kasashen Afirka ta Yamma na fama da matsananciyar yunwa, adadin da ake hasashen zai karu a 'yan watannin da ke tafe musamman a kasashen Najeriya da Nijar da Mali da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/49V5j
Hunger in Somalia Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasashen yankin yammacin Afirka na fuskantar karancin abinci da ba a ga irin shi ba a tsawon lokaci, wanda ke da nasaba da tashe-tashen hankula da fari da ma na baya-bayan nan rikicin da ke tsakanin kasashen Ukraine da Rasha da ya haddasa tsadar kayayakin masarufi da ma karancinsu. A cewar wani rahoto da kungiyar OXFAM ta fidda a wannan Talatar.

Yanzu haka akwai sama da mutane miliyan 27 da ke fama da matsananciyar yunwa a yankin kuma adadin zai karu ya zuwa miliyan 38 nan da watan Yunin da ke tafe, Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata an sami kari na kaso 40 cikin dari.

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar gami da Najeriya da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda da suka hana al'umma ayyukan gona na daga cikin kasashen da yunwa za ta fi ta'azzara.