1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yankin tafkin Chadi sun yi taro kan tsaro

Umaru AliyuOctober 13, 2014

Ministocin kasashe biyar masu makwabtaka da Najeriya kusa da tafkin Chadi sun yi taro domin nazarin matakan tsaro a tsakaninsu da hanyoyin yaki da kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1DV6S
Frankreich Sicherheitskonferenz in Paris Kamarun Nigeria Paul Biya und Goodluck Jonathan
Hoto: picture-alliance/AA

Ministocin harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen guda biyar da suka hada Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Chadi, Kamaru da kuma Jamhuriyar Benin sun cimma wannan matsaya ne da a yanzu za su mika kudurin gaban kungiyyar tarayyar Afrika da kuma Majalisar Dinkin duniya, wanda sai sun yi hakan ne za su iya samun hallacin kafa runduna ta musamman don yaki da aiyyukan ta'adanci a tsakaninusu.

Ambassada Aminu Wali shine ministan kula da harkokin kasashen waje na Najeriya. Ya bayyana muhimmancin wannan kuduri da suka samu cimmawa.

"Dama can sojojin kasashen gaba daya suna yaki da 'yan tawayen Boko Haram da suka dame su, amma ba za mu iya samun amincewa na duniya gaba daya, mu ci gaba da wannan yunkuri namu ba sai mun samu amincewa daga Majalisar Dinkin Duniya. A bisa doka, duniya ta san cewa in wani abu ya taba daya to ya taba dukkaninmu ne."

A lokutan baya dai an san cewa akwai kasashen da ke nuna ja baya a wannan tafiya da ta sanya gudanar da tarurruka iri dabam-dabam don dinke baraka, ko a yanzu tun da sun tsara shirin a karkashin kasashen dake tafkin Chadi sun kawo karshen matsalar? Malam Sunusi Imran Abdullahi shine sakataren gudanarwa na hukumar kula da tafkin Chadi.

Nigeria Soldaten Boko Haram ARCHIVBILD
Farautar 'yan kungiyar Boko HaramHoto: Reuters

‘'Tun kusan watani bakwai da suka gabat kullum muka yi taro sai mun samu Karin hadin kai, dama ai kasar Kamaru ce, mun samu ci gaba a taron da muka yi ranar bakwai ga watan nan. Kana nan ai ministan tsaron kasarsu yace ga wakilin shin an kuma ya bashi duk hadin kan daya kamata''.

Koda yake ministocin kasashen na murnar kaiwa ga wannan matsayi da suke ganin a yanzu sun dinke baraka da tasa taba kasa daya tamkar taba dukkaninsu guda biyar ne, don zasu yi taron dangi a kan kowace irin matsala to sai dai sanin cewa Amirka na adawa da sayarwa Najeriya makamai ko ya za su bullowa tunkurar Majalisar Dinkin Duniya? Har ila yau ga Ambasada Aminu Wali.

‘'Na yarda Amirka da sauran kasashe biyar sune wakilai na din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kuma in sun ce sun ki shikenan, amma kada a yi la'akari da wannan domin wannan kuduri da zamu kai majalisar dinkin duniya bai bude kofa ga wata kasa da za ta shigo mana ba, sai in ka bada kafa ga wata kasa da ke da gilla a kanmu ko wata kasar da ke cikin wadannan shine in ka bada kafa zata shigo''

Na yi kokarin jin ta bakin wakilin kasar Nijar a taron, Bazzum Muhammad, wanda yaki cewa komai duk da matsin lambar da na yi mashi.

Nordkamerun Grenzregion zu Nigeria Mandara Berge
Iyakar Najeriya da Kamaru: maboyar 'yan kungiyar Boko HaramHoto: AFP/Getty Images

An dai yanke shawara za a girka wannan runduna ta kasa da kasa a garin Baga Kawa da ke jihar Borno a Najeriya, domin wannan aiki. Abin jira shine ganin tasirin rundunar, musamman saboda yadda matsalar rashin tsaro ta jefa daukacin rayuwar al'ummar yankin arewa maso yammacin Najeriya a yanayi na babu babba ba yaro.