Hulda na karfafa tsakanin Rasha da Afirka
February 6, 2024Za a iya cewa sabon kawance da aka kulla tsakanin Rasha da gwamnatin mulkin soji a Ouagadougou na tafiya sau da kafa, inda hakan ya fito karara bayan aikewa da makaman yaki da Rasha ta yi da ma shan alwashin kare shugaban rikon kwaryar Burkina Faso Kyptain Ibrahim Traoré da kuma al'ummar kasar baki daya. Nan gaba kadan ake sa ran tawagar dakarun Wagner 100 da ke kasar za ta karu ya zuwa 200. A cewar jagoran sojin kasar babu wani sojin Wagner da ke a fagen yakin, sai dai bai kawar da yiwuwar samunsu a nan gaba ba kamar yadda ya ke kokarin kawar da jita-jitar cewar suna taimaka musu yaki da mayakan jihadi, Kyaptin Traore wanda ya nanata cewar sojojin Rasha da ke a kasar yanzu haka masu horas da sojojinsu ne. A cewar wani dan kasar Nestor Podasse da ke kare gwamnatin sojin ya ce ai wannan ba sabon abu ba ne idan sojoji suka zo don nuna yadda za yi amfani da kayakin yaki da aka sayo daga wajen su. ''Gammayya ce ta aiki kafada da kafada tsakaninmu da Rasha,babu wasu kamfanonin na daban yanzu haka a cikin kasar nan, sojojin Rasha ne za su horas da sojojinmu yadda za su yi amfani da makaman da muka sayo daga wajensu, kuma wannan ba wani sabon abu ba ne.''
Manufofin Rasha a kasashen Afirka na da fuskoki da dama
Wannan sabuwar alaka da Rasha ta kulla da kasashen Afirka, na nuna yadda Shugaba Vladmir Putin ke kara nuna kasancewarsa a nahiyar, musamman ma a kasashen yankin yammaci na Sahel. to sai dai a c ewar masaniyar tarihi Irina Filatova sojojin na Wagner za su bazu a tsakanin kasashen biyar da suka hada da Burkina Faso da tuni suka ciki da Mali da Nijar da Libiya har ma da Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya."Manufofin Rasha a kasashen Afirka na da fuskoki da dama, akwai yada farfagandar siyasarta da kuma kokari na fadada kasuwancinta da wasu tsare-tsare, zai yi matukar wahala a sami wata manufa da Rasha za ta yada a wadannan kasashe da ta shiga ba tare da samun ribar ta ba"
Sojin Rasha za su kafa sansani soji a Afirka
Tun a shekarar 2018 Rasha ke baza komarta a nahiyar Afirka, a wancan lokacin sun samar da wata yarjejeniya tsakaninsu da mahukunta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta samar da sansanin soji da ma bai wa sojojin Wagner wata muuhimmiyar rawa ta yaki da 'yan tawaye da suka addabi kasar.