Kenya ta dauki hankalin jaridun Jamus
September 22, 2017Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta labari mai taken " kundin tsarin mulkin kasar Kenya na cikin rikici". Ta ce a ranar Alhamis ce hukumar zaben kasar ta sanar da matsar da ranar da za'a sake gudanar da zaben shugaban kasa da karin kwanaki tara, inda a yanzu ta ce zaben zai gudana ne a ranar 26, a maimakon ranar 17 da aka sanar tun a baya.
Hukumar na mayar da martani ne kan sukan zaben da kotun kolin wannan kasar ta gabashin Afirka ta yi. Daya daga cikin misalan mishkila da zaben ya fuskanta a cewar kotun, shi ne rashin takardun masu kada kuri'a wajen dubu 11 daga cikin adadi mazabu dubu 44 da ke fadin kasar,
Dan takara daga bangaren adawa Raila Odinga ya zargi tabka magudi da arongizon kuri'u a bangaren shugaba Uhuru Kenyatta, duk kuwa da cewar babu shaidar fasa kwaurin sakamakon ta yanar gizo.
Kwaskware kundin mulki ya ci tura a Yuganda
An tashi baram-baram a zaman muhawarar majalisar dokokin Yuganda da aka dade ana jira kan batun gyaran kundin tsarin mulkin kasar domin rage wa'adin shekaru na takarar shugabancin kasar. Da haka ne jaridar Die Tageszeitung ta bude sharhin da ta rubuta kan halin da ake ciki na ci gaba da dauki daidai da ake wa 'yan adawa a kasar ta gabashin Afirka.
Tun a ranar Litinin ne dai jam'iyyun adawa da kungiyoyin kare hakkin jama'a da masu zaman kansu suka kaddamar da gangamin adawa wadda ta faro tun daga jami'ar Makerere da ke birnin Kampala, inda aka kama dalibai 10. A cewar rundunar 'yan sandan kasar dai kamen na da nasaba da yadda wasu bata-gari ke amfani da irin wannan damar wajen aikata miyagun aiki.
An dai girke jami'an tsaro kama daga sojoji da 'yan sanda a sassa daban- daban na kasar gabannin zaman majalisar na ranar Alhamis, domin sauya sashin kundin tsarin mulkin da yayi tanadin cewar, shugaban kasa ba zai shige shekaru 75 akan mulki. Hakan na nufin shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 73 ba zai iya takara a shekara ta 2020 ba, idan har ba'ayi gyaran wannan doka ba.
Sharhi kan hular lauyoyi da alkalan Afirka
Jaridar Süddeutsche Zeitung kuwa ta duba batun al'adar nan ce ta amfani da hular gashi ta lauyoyi da alkalan da ke kasashen renon Ingila. A cewarta duk da yanayi na matsanancin zafi da wasu kasashen Afirka ke ciki, wannan rukuni na mutane na ci gaba da daraja wannan al'ada da suka gada daga Birtaniya wadda ta yi watsi da ita.
Kama daga Kenya zuwa Najeriya da Zimbabuwe, da wuya kaga alkali ya zartar da hukunci ba tare da ya sanya wannan hular gashi ba. Chioma Unini da ke zama lauya a Najeriya ta ce yanayi da al'adar wadanda suka kirkiri hular gashi ya sha banban da namu.
Shi ma shugaban hukumar lauyoyin kasa da kasa na Afirka kuma dan Zimbabwe Arnold Tsunga, cewa ya yi wannan al'adar bata dace da mu ba. Ya jima yana fafutukar ganin cewar an haramta amafani da hular gashin da turawan mulkin mallaka suka tilasta alkalan kasashen amfani da ita.