Kila-wa-kala kan takarar Sonko a Senegal
July 5, 2023Makomar madugun 'yan adawa Ousmane Sonko a fagen siyasar Senegal ta dogara ne kam tafarkin shari'a. Hasali ma hukuncin da kotu ta yanke a kansa na iya zama wani kalubale ga manufofinsa na tsayawa takara a zaben shugaban kasa, ko da yake an yanke masa hukuncin ne ba tare da ya bayyana a gaban kotun ba. Wannan ne ma ya sa jam'iyyar Pastef ta Sonko ke ganin cewa akwai sauran rina a kaba.
Diallo Diop da ke zama mataimakin shugaban jam'iyyar Pastef ya ce: "Har yanzu tana kasa tana dabo game da batun hukuncin kotu domin ta yanke masa hukuncin ne ba tare da halartarsa ba. Da zaran ya sake bayyana a gabanta kotun za ta karya shara'ar a sake yin wata, akwa batun wa'adin daukaka kara da ya saura."
A watan Fabrairun 2024 ne za a gudanar da babban zaben na kasar Senegal ciki har da na shugaban kasa, Sai dai a watan Agustan 2023 ne za a soma tattara takardun samun amincewar 'yan jam'iyya domin tsayawa takara kamar yadda dokar kasar ta tanada, Sai dai ayar tambayar ita ce, jam'iyyar Sonko na da yakinin samun wannan damar? Diallo Diop ya ci gaba da cewa: "Ba makawa lokaci na kara kure mana. Ba wai ga masu zargi da ke tuhumarsa da amfani da matasa ba, amma duk wani alkalin da ke sauraren kara na kirki zai yi watsi da wannan tuhumar a kwandon shara."
Jam'iyyar Pastef na ci gaba da nacewa kan jagoranta cewa bai taba aikata wani babban laifin da zai hana masa shiga takara a bbabban zaben da ke tafe ba, duk da fargabar da ke da akwai na yiwuwar kama shi a gabanin zaben. Ga masu sharhi kan harkokin siyasa na kasa da kasa irin su Dr Dicko Abdourahmane na ganin cewa rashin Sonko a fagen zaben ba zai taba samarwa kasar Senegal kwanciyar hankali ba.
A watan Satumban 2023 ne jam'iyyun siyasa na Senegal da ke sha'awar tsayar da 'yan takara za su gabatar da jerin sunayen su a gaban hukumar zabe. Sai dai ana kallon cewa zaben zai kasance mai cike da cece-kuce a fagen dimukuradiyyar kasar Seenagl.