1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shirin kwashe majinyata daga Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
November 16, 2023

Majalisar Dinkin Duniya na neman hanyoyin da za ta kwashe mutane daga asibitin Al Shifa, amma zabinta takaitacce ne a bangaren tsaro da kuma matsalolin kayan aiki.

https://p.dw.com/p/4Ysem
Nahostkonflikt - Schifa-Krankenhaus
Hoto: Khader Al Zanoun/AFP

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ba ta da isasshen man fetur a motocin daukar marasa lafiya don kwashe majinyata, kamar yadda darektan agajin gaggawa na WHO Rick Brennan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Masar ta bayyana aniyarta na bada tallafin motocin daukar marasa lafiya zuwa Gaza don kwashe mutane, muddin za a iya samar da tabbacin tsaro domin shigewarsu ba tare da wata matsala ba, in ji shi a wata hira daga birnin Alkahira.

Hukumar lafiyar ta duniya ta fahimci cewa, har yanzu akwai majinyata kusan 600 da suka hada da 27 da ke cikin mawuyacin hali a asibitinShifa, wanda sojojin Isra'ila suka afkawa cikin wannan makon, bayan kawanyar da suka yi wa asibitin na kwanaki, in ji Brennan.