1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin mayar da hukumomin gwamnati daga Abuja zuwa Legas

January 19, 2024

A wani abun da ke zaman alamun sake komawa gidan jiya, a karo na biyu cikin makonni biyu ana kallon kokarin mayar da hukumomin gwamnatin tarrayar Najeriya zuwa birnin Legas dake zaman tsohuwa ta cibiyar mulki ta kasar

https://p.dw.com/p/4bThI
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a Abuja
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a AbujaHoto: public domain

A cikin makon da ya shude ne dai wata sanarwar cikin gidan babban bankin Najeriyar CBN ta ce bankin zai mayar da wasu sassansa zuwa birnin Ikko domin cigaba da aiyyukansu a can. Kafin kuma a karshen wannan makon ita ma hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta bi sahu tare da ayyana shirin komawa Ikkon bisa hujjar wurin watayarwar aiki. Matakan kuma da suka fara daukar hankali, kasar da cunkoso ya tilasta wa gina sabuwar hedikwatar mulki, amma kuma ke neman komawa cunkoson.

Duk da cewar tun a shekarar 1976 ne aka ayyana kafa birnin Abuja domin maye gurbin na Ikko wajen zama cibiyar mulki, da kyar da gumin goshi gwamnatin Ibrahim Babangida ta dauke cibiyar mulkin daga Ikko ta kawo ita Abujar a 1991.

Kokarin adabo da Abujar dai a tunanin Sanata Umar tsauri jigo a jam'iyyar PDP ta adawa na da kammani da kokarin cika buri na kabila. Kuma ko bayan batun siyasa ana kallon sabon matakin na iya tasiri ga tattalin arzikin Najeriyar.

Cunkoson dai na tasiri ga hada hadar kasuwanci dama kokarin fitar da kaya zuwa kasashen waje daga birnin Ikkon. Kuma karin ma‘aikatan gwamnatin na iya dada cunkushe lamura a tunanin Dr Isa Abdullahi kwararren masanin tattalin arziki a Najeriyar.

Sai dai koma yaya take shirin kayawa tsakanin masu tunanin babu hankali a matakin gwamnatin da masu ikirarin neman sauki, ba doka a tunanin Barrister Saidu Mohammed Tudun Wada dake zaman wani lauya mai zaman kansa, Najeriyar da ta tanaji ajiye ma‘aikatu da hukumomi na gwamnatin a Abuja.

Tun ma kafin Najeriyar dai kasashe irin su Brazil da Masar da ma Amurka,sun sauya mazaunin cibiyar mulkin kasashensu, ko dai bisa batu na tattali na arziki kok o tsaron dake da tasirin gaske