Kokarin sasanta manoma da makiyaya a Najeriya
October 19, 2017Manufar matakin hakan dai yanzu a cewar shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Filato Nura Abdullahi, shi ne don tabbatar da samun hadin kai tsakanin Fulani makiyaya tare da sauran kabilun jihar baki daya. Taron wanda ya kankama a garin Wase, tare da kaddamar da wani hasashen gina ofishin kungiyar makiyayan na Wase, ya hado al'ummomi tare da shugabanin Fulani makiyaya da kuma Ardo-Ardo da suka fito daga yankunan Shendam da Quaan Pan da Mikang Kanem da Langtang da dai wasu yankunan.
Wannan mataki na shugabanin kungiyar ta Miyetti Allah dai wani yunkuri ne wanda zai ci gaba inda kungiyar ta ce za ta kara azama wajen ganin ta shirya tarurukan zaman lafiya da samun hadin kai tsakanin 'ya'yanta da sauran kabilun jihar a duk inda suke.
Masu lura da al'amura dai sun lura cewa wannan mataki da kungiyar ta Miyetti Allah ta dauka game da samun hadin al'ummomi baki daya, abu ne da ya zo dai dai lokacin da ake bukata, biyo bayan irin yanayi da jihar ke neman shiga na tashen-tashen hankula, bayan zaman lafiya da aka soma samu a yan shekarun baya.