Koma baya a yaki da cin hanci a Najeriya
February 22, 2018Rahoton na kungiyar Transparency International da ya yi nazari a kan matsalar cin hanci da rashawa a kasashe 180 na duniya ya nuna yadda wasu kasashe suka fuskanci koma baya, inda a 2017 Najeriya ta samu maki 28 abin da ya sanya ta zama matsayi na 148 daga cikin kasashe 180 da ta sanya ido a kansu. Wannan ya nuna koma baya daga matsayi na 136 da kasar ta samu a 2016. Kungiyar dai ta ce duk da samun nasarar kwato makudan kudade da kame mutane da dama da aka yi bisa zargin cin hanci, har yanzu Najeriyar ba ta iya hukunta wani fitaccen mutum ba daga jerin kararraki 286 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gabatar a kotu, kuma babu sahihin tsarin yadda ake kula da kudaden da aka kwato, abin da ke jefa tsoro na sake wawushe su. Koda yake wannan matsayi na cin hanci da kungiyar ta fitar ya sanya jefa tababa a zukatan jama'a da dama musamman a game da ci-gaban da aka samu a wannan fanin, amma Transparency International tace Najeriya na asarar kashi 25 cikin 100 na karfin arzikinta a fannin cin hanci.
Jami'an tsaro na cin zarafin dan Adam
Rahoton na Transparency International dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ita ma kungiyar Amnesty International ta fitar da nata rahoton da ke nuna damuwa a kan yawan take hakokin dan Adam da kashe-kashe babu dalili da take zargin sojojin Najeriyar da aikatawa. Abin jira a gani shine matakin da hukumomin Najeriya zasu dauka a kan wadannan rahotanni da a lokutan baya sukan musanta zarge-zargen, koda yake a yanzu sun kai ga kafa kwamitin binciken da ake jiran matakin da za a dauka a kan batu.