1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafi kan hana amfani da hijabi a jihar Legas

February 1, 2019

A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke mutunta ranar amfani da hijabi a duniya, wasu musulmi masu amfani da hijabin a jihar Legas ta Najeriya sun damu ne da matakan mahukunta dangane da wannan sutura.

https://p.dw.com/p/3Caba
Südafrika Muslima mit Hijab
Hoto: Getty Images/AFP/G. Khan

A yayin da ake gudanar da bikin a sauran kasashen musulmi a duniya, a Najeriya musamman a yankin kudu maso yammacin kasar kokawa musulmin ke yi dangane da yadda ake hana amfani da hijabi musamman ga yaya mata a makarantun gaba da firamare duk da cewa gwamnati ta amince da hakan.

A wani taro na nuna kin amincewa da matakin, shugaban kungiyar kare manufofin musulmi a Najeriya, farfesa Ishaq Akintola, ya shaida wa manema labaru a birnin Legas cewa matakin da shugabannin makarantu ke dauka, ya saba wa dokar da ta amince da amfani da hijabi ga dalibai.

Farfesa Akintola, ya bayyana wasu makarantu a cikin jihar Legas da cewa sun yi kememe na bin dokar da gwamnati ta sanya na amfani da hijab duk kuwa da cewa za su bi kadin hakan bisa adawa da shugabannin makarantun. Ya dai bukaci kafa kwamitoci na musamman a duk masallatan da ke yankin don tabbatar da bin amfani da hijab a yankin baki daya.

Sakatare Janar na kungiyar ta kare muradun musulmin, Alhaji Hakeem Williams, ya ce abin takaici ne yadda ake kallon mace tamkar koma baya duk da matsayin ta na Uwa ga kowa da kowa.

Malama Zainab Umar, wacce take sanya hijab ta ce batu na gaskiya shi ne amfani da suturar umarni ne daga Allah, saboda haka babu gudu ba ja da baya wajen ci gaba da fadakar da ‘yan uwanta mata kann amfani da hijabi a Najeriyar baki daya .

A yanzu haka dai kungiyar na tutiyar cewa babu hijabin ga mata to kuma babu kuri’a a zaben kasa da ke karatowa.