1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Koriya ta Arewa za ta cika alkawarin da ta yi wa Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 14, 2024

Mr Kim Jong Un na jaddada alkawarin ne lokacin da ya karbi bakuncin sakataren majalisar kula da harkokin tsaron Rasha

https://p.dw.com/p/4kcaA
Nordkorea Russland Putin bei Kim Jong Un
Hoto: GAVRIIL GRIGOROV/AFP/Getty Images

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya sha alwashin karfafa dangantaka da Rasha ta ko wane fanni, tare da dabbaka yarjejeniyar da suka kulla da juna a cikin watan Yunin da ya gabata, duk kuwa da matsin lambar da suke fuskanta kan yakin da Rasha ke yi da Ukraine.

Karin bayani:Putin zai kai ziyara Koriya ta Arewa

Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mr Kim Jong Un na jaddada wannan alkawari ne lokacin da ya karbi bakuncin sakataren majalisar kula da harkokin tsaron Rasha Sergei Shoigu a fadarsa.

Karin bayani:Zargin musayar makamai tsakanin Putin da Kim Jong Un

A cikin watan Mayun da ya gabata ne shugaba Vladimir Putin na Rasha na ya sauke Sergei Shoigu daga matsayinsa na ministan tsaro, sannan ya ba shi sabon mukamin sakataren majalisar kula da harkokin tsaron, wanda ake wa kallon babban na hannun damansa.