Alakar Rasha da Koriya ta Arewa ta girgiza Koriya ta Kudu
October 25, 2024Koriya ta Kudu ta bayyana matukar damuwa bayan amincewa da wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Rasha da makwabciyarta kuma abokiyar gabarta Koriya ta Arewa, yayin da shugaba Zelensky na Ukraine ke kiran abokan huldarsa na Yamacin Duniya da su gaggauta ladabtar da wadannan kasashe biyu.
Karin bayani: 'Yan majalisa a Rasha sun amince da yarjejeniyar tsaro da Koriya ta Arewa
A cewar shugaban na Ukraine, sojojin Koriya ta Arewa za su fara dafa wa takwarorin na Rasha a fagen yaki daga ranar Lahadi mai zuwa, yana mai bayyana fargabar rincebewar al'amura bayan barkewar rikici tsanakin kasarsa da Rasha yau da watanni 32.
A nata bangare Koriya ta Arewa yayin da take martani a ranar Juma'a, ta ce idan har za ta tura sojojinta zuwa Rasha sai ta tabbatar ko hakan bai saba wa dokokin kasa da kasa ba, sai dai amma ba ta ba da tabbaci ko karyata zargin cewa ta tura ko tana shirin tura sojojin nata zuwa Rasha ba.