Tsare tsohon gwamnan Jigawa a Najeriya
May 2, 2017A Dutse babban birnin jihar Jigawa dai tsohon gwamnan jihar Alhaji Sule Lamido ya fuskanci kuliya sakamakon zargi na kokarin tada hankalin al'umma, a yayin kuma da a can a Minna fadar gwamnatin jihar Neja aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Muazu Babangida Aliyu a bisa zargin halin bera. Shi ma dai dan uwansa da ya jagoranci jihar Benue a karkashin jam'iyyar PDP Gabriel Suswam ya share kusan tsawon wata guda yana bakuntar hukumar tsaron cikin gidan ta DSS a bisa zargi na mallakar makamai. Duka tsofaffin gwamnonin guda uku dai na zaman jiga-jigan jam'iyyar PDP ta adawa a kasar. Abun kuma da ya tada hankalin jam'iyyar da ta bara ta kuma ce ana yi mata dauki na dai-dai a bangaren na hukumomin kasar saboda siyasa.
PDP dai ta ce akwai batu na siyasa game da yadda ake bi ana cafke jagorori na adawa na kasar a bisa laifukan da ke kama da mafarkin rana, maimakon sabawa doka a kasar. Dr Umar Ardo dai na zaman jigon jam'iyyar na kasa da kuma ya ce ana kokarin fesa turare na laifuka ga 'ya'ya na gwamnatin, a yayin kuma da ake neman hallaka 'yan adawa da maganin kashe kwari. Kama daga tsohon sakatare na gwamnatin ya zuwa babban jami'i na leke na asiri dai, sun kare ne da kafun kwamiti maimakon gurfanar da su gaban kuliya gadan-gadan, yayin kuma da aka kai ga wanke babban jami'i na mulkin fadar a cikin wani zargin hancin da ya dauki lokaci cikin kasar. To sai dai kuma a fadar Abubakar malami da ke zaman ministan shari'ar Tarrayar Najeriyar kuma jagoran yakin tabbatar da gaskiya da adalci a kasar, matakin na gwamnati bashi da sani balle kuma sabo da wani. Abun jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin gwamnatin da ke fadin ta taba kowa da kuma masu adawar da ke kirarin 'yan mowa da na bora.