SiyasaAfirka
Kotu ta ce a bude asusun bankin 'yan #EndSars
February 10, 2021Talla
A wannan Larabar ce kotun da ke Abuja a ta bakin alkali Ahmed Mohammed, ta bayar da umarni ga babban bankin Najeriya da ya gaggauta bude asusun ajiyan masu zanga-zangar #EndSars da aka toshe a bara. Wadanda lamarin ya shafa na daga cikin jagororin zanga-zangar da suka ja ra'ayoyin jama'a a ciki dama wajen kasar.
Umarnin ya biyo bayan cimma matsaya da aka yi, a tsakanin bangaren gwamnati da bangaren wakilan masu zanga-zangar, da zummar rufe babin kazamin rikicin da ya janyo asarar rayuka da salwantar dukiyoyin jama'a da ma na gwamnati kan adawa da jami'an gwamnati da ake zargi da cin zarafin fararen hula.